Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-18 08:44:44    
Ana gudanar da aikin share fage na gasar wasannin Asiya ta Guangzhou yadda ya kamata

cri

Birnin Guangzhou shi ma yana son shirya gasar wasannin Asiya mai tsarin musamman na kasar Sin wadda za ta nuna halayen musamman na lardin Guangdong da birnin Guangzhou. Kamar yadda aka saba, dukkan gasar da aka shirya cikin wata nahiya, ko da yaushe kasashe masu saukar baki kan mai da hankali kan aikin kirkire-kirkire da na nuna al'adun tsarin musamman. A halin da ake ciki yanzu, an riga an kawo karshen aikin share fage na mataki na farko, muna fatan za a kara jin dadin kallon bikin budewa da rufe gasar wasannin Asiya da bikin ba da yabo ga 'yan wasa. Ban da wannan kuma, kwamitin shirya gasar na Guangzhou ya tsai da cewa, za a yi nune-nunen wasannin motsa jiki mai tsarin musamman na birnin kafin gasa ko a yayin gasa. A waje daya kuma, za a yi kokari don kyautata aikin samar da hidimar abinci da muhallin saukar baki, ta yadda za a sa masu halartar gasar su kara jin dadin zaman rayuwa a cikin halin al'adu iri na tsarin musamman na kasar Sin. Gu Shiyang ya karfafa cewa, cudanya tsakanin al'adun Asiya da al'adun kudancin kasar Sin ita ce aikin kirkire-kirkiren da muke yi. Ya ce:  "Mun fi mai da hankali kan cudanyar al'adun Asiya, dalilin da ya sa haka shi ne domin Asiya babbar nahiya ce wadda ke da al'adu iri daban daban. Idan ana son kafa Asiya mai zaman jituwa, to, dole ne a nuna biyayya ga al'adu daban daban kuma a yi kokarin samun cudanyarsu. A yayin wannan gasar wasannin Asiya, muna son kara yin farfaganda kan al'adun 'Lingnan' wato kashi daya dake cikin al'adun kasar Sin. "

Gu Shiyang ya yi mana bayani cewa, yanzu ana gudanar da aikin share fage na gasar wasannin Asiya lami lafiya, kuma za a fara aikin yin hayar masu aikin sa kai daga watan Yuni na bana. Ban da wannan kuma, an kimmanta cewa, za a kammala aikin gina cibiyar wasannin Asiya ta Guangzhou a watan Agusta ko Oktoba na bana. Kan batun gina dakuna da cibiyoyin wasanni, Gu Shiyang ya fayyace cewa, an gina sabbin dakuna da cibiyoyin wasanni 12, kuma za a gyara ko habaka wasu tsoffin dakuna da cibiyoyin wasanni, saboda mazauna Guangzhou sun saba motsa jiki kowace rana, shi ya sa dole ne gwamnatin birnin Guangzhou ta yi la'akari kan bukatun jama'ar birnin. Gu Shiyang ya ce:  "Za mu fara aikin gyara tsoffin dakuna da cibiyoyin wasanni nan gaba, yanzu yawancin mazauna birnin Guangzhou suna motsa jiki a cikin wadannan dakuna da cibiyoyin wasanni, shi ya sa za mu zabi lokacin yin gyara mai dacewa."

1 2 3