Ran 1 ga watan Yuli na shekarar 2004, majalisar wasannin Olympic ta Asiya ta sanar da cewa, birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin ya sami iznin shirya gasar wasannin Asiya a karo na 16, daga nan birnin Guangzhou ya zama birnin kasar Sin na biyu da ya sami iznin shirya gasar wasannin Asiya a bayan birnin Beijing. Wannan ita ma wata babbar gasa ce ta daban da birnin kasar Sin zai shirya tun bayan da aka sami nasarar shirya gasar wasannin Olympic a birnin Beijing a shekarar 2008. Kamar yadda kuka sani, za a bude zama na 16 na gasar wasannin Asiya a shekarar 2010, yanzu dai, saura kusan shekara daya ke nan dake gaba, kuma ana gudanar da aikin share fage na gasar yadda ya kamata. Kwanakin baya ba da dadewa ba, wakilinmu ya ziyarci mataimakin babban sakataren kwamitin shirya gasar wasannin Asiya ta Guangzhou kuma mataimakin babban sakataren kwamitin birnin Guangzhou Gu Shiyang domin jin ta bakinsa. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayanin kan wannan.
Tun bayan da aka sami iznin shirya gasar wasannin Asiya ta karo na 16, a kullum gwamnatin birnin Guangzhou da kwamitin shirya gasar wasannin Asiya na birnin suna dora babban muhimmanci kan aikin koyon fasahohin da aka samu yayin da ake shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing. A shekarar 2006, an kafa kwamitin shirya gasar wasannin Asiya ta Guangzhou, daga baya kuma, bi da bi an tura wakilai zuwa Beijing sau biyu domin su yi aiki a cikin kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing. A yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing, jami'an sassa daban daban na gwamnatin birnin Guangzhou su ma sun zo Beijing domin kara fahimtar fasahohin gudanar da harkokin birni a yayin gasa. Gu Shiyang ya kyautata tunani da cewa, birnin Beijing ya shirya gasar wasannin Olympic lami lafiya kuma ya sami cikakkiyar nasara, wannan ya nuna cewa, kamata ya yi a gudanar da harkokin birni tare da kwamitin shirya gasa. Ya fi kyau birnin Guangzhou ya koyi fasahar da Beijing ya samu kan wannan batu. Ya ce: "Gwamnatin birnin Beijing ta dauki hakkin gina dakuna da cibiyoyin gasar wasannin Olympic bisa wuyanta, ban da wannan kuma, gwamnatin birnin Beijing ita ma ta dauki hakkin kiyaye muhalli da kwanciyar hankalin birnin bisa wuyanta, haka kuma, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ya kula da aikin sana'a na gasar kawai."
1 2 3
|