Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-17 18:54:36    
Jin dadi a filin wasan Skiing wato gudu a kan faifan musamman ko allo a tsakanin duwatsu a Kanasi ta jihar Xinjiang

cri

Kamar yadda take fada, Zheng Libo, wani mai yawon shakatawa da ya zo shiyyar Kanasi daga garinsa na birnin Jilin, shi ma ya samu abubuwa da yawa. Yana mai cewar, "A da ban taba ganin irin wannan gasa ba. Wannan gasar wasan skiing mai dogon tarihi ta sa mu tunani da yawa. Tun can da, mutane sun fara farauta da gudu a kan faifan musamman ko allo a tsakanin duwatsun dusar kankara, su yi gwagwarmaya da muhalli domin kasancewa a duniya. A sakamakon kallon wannan gasa, mun iya kara samun fahimta kan yadda aka yi a can can can da. "

A sakamakon shirya shagalin daukar hoton, ni'imtattun wurare da al'adun tarihi da al'adun kananan kabilu da kuma wuraren da ke shafar al'adun mutane da aka samu a shiyyar Kanasi a lokacin hunturu sun shahara ne cikin gajeren lokaci a jihar Xinjiang da ma duk fadin kasar Sin. Yanzu dogon lokacin hunturu ya samar wa mutane karfi. Zhang Zhili, wani mazaunin birnin Beijing ya bayyana cewa,"A ganina, ya kamata mu kiyaye irin wannan abun tarihi na al'adu, wanda ya sa kaimi kan kyautata ingancin manoma da makiyaya da kuma kiyaye albarkatun al'adun yawon shakatawa."

Wang Yitao, shugaban hadaddiyar kungiyar wasan skiing ta kasar Sin ya taba kallon wasannin kankara a sassa daban daban na duniya, amma a karo na farko ya ga irin wannan gasar wasan skiing mai dogon tarihi. Ya nuna cewa,"Ba kawai mazauna shiyyar Aletai da ta Kanasi suna mallakar irin wannan gasa ba, har ma duk jama'ar Sin ne ke mallakarta. Ina fatan za a iya raya ta yadda ya kamata, ta haka karin mutane za su zo nan, za su nuna sha'awa kan wannan wuri, wanda ke matsayin wurin yawon shakatawa ga jama'ar Sin da ma ta duniya."

An dai sani cewar, gani ya kori ji! In kuna sha'awar gudu a kan faifan musamman ko allo a tsakanin duwatsu, to, kuma iya zuwa shiyyar Kanasi a lokacin hunturu domin yin wasa da dusar kankara.


1 2 3