Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-17 18:54:36    
Jin dadi a filin wasan Skiing wato gudu a kan faifan musamman ko allo a tsakanin duwatsu a Kanasi ta jihar Xinjiang

cri

A gun bikin bude shagalin daukar hoton da aka yi a wannan shekara, an shirya wasu harkoki masu kayatarwa da mazauna wurin su kan yi a kan dusar kankara da kuma kankarar kanta. Ko da yake yawan zafi ya kai digiri sentigrade 30 ko fiye a kasa da sifiri, amma masu sha'awar daukar hoto da matafiya sun dauki hotuna da bidiyo ba tare da tsayawa ba. Ju Xingzhou ya zo shiyyar Kanasi har sau 6 daga garinsa na birnin Shanghai, amma a karo na farko ne ya yi bulaguro a nan a lokacin hunturu. Ya ce,"Na samu karfi a shiyyar a sakamakon abubuwan da suke kasancewa kamar yadda suke ciki a can da. Na cika burina a wannan karo, ina zuwa nan ziyara ne a duk lokacin bazara da na zafi da na kaka da kuma na hunturu."

Baya ga more kallo a wurare masu ni'ima, gasar yin farauta kan faifan musamman ko allo a tsakanin duwatsun dusar kankara mai dogon tarihi da ba a iya ganin irinta a sauran wurare ita ce abun da ya fi jawo sha'awar mutane. Bisa ka'idojin gasar, tsawon hanyar gasar ya kai kilomita 18, inda a kan yada zango a ko wane kilomita 6. 'Yan wasa kan harba takobi ga dabbobin jabu da aka kera da fata da gashin dabbobi. A karshen gasar, duk wanda ya fi sauri wajen harba kibiya mafi daidai zai iya zama zakara.

Bisa nazarin da masana suka yi, an ce, shiyyar Aletai da ke kuryar jihar Xinjiang ta arewa ita ce mafarin wasan skiing na dan Adam. Bisa zane-zanen da aka yi kan duwatsu game da yadda ake gudu a kan faifan musamman ko allo a tsakanin duwatsu a can can can da, an ce, yau da shekaru dubu 10 da suka wuce, makiyaya mazauna shiyyar Aletai su samar da wani faifan musamman da katako da fatun dabbobi, wanda kuma kawo yanzu dai ake ci gaba da amfani da shi.

A tsakar ranar bikin bude shagalin, 'yan wasa fiye da 30masu sanye da tufafin kabilarsu sun sa irin wannan faifan musamman mai dogon tarihi a kafarsu, su ja keken tafiya a kan kankara da suka kera da fatun dabbobi, su yi tafiya a tsakanin manyan duwatsun da dusar kankara ke mamayewa. Ingantacciyar fasaharsu ta wasan skiing tana ba matafiya da 'yan kallo mamaki sosai. Wu Fengxia, wadda ta zo ne daga birnin Urumchi ta gaya mana cewa, "Na samu karfin zuciya sosai saboda ganin jama'ar wata kabila ta iya kiyaye al'adunsu na gargajiya yadda ya kamata kamar haka. Ina matukar Alla-Alla wajen yin gwaje-gwaje. Na yi farin ciki kwarai da gaske."

1 2 3