Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-17 18:54:36    
Jin dadi a filin wasan Skiing wato gudu a kan faifan musamman ko allo a tsakanin duwatsu a Kanasi ta jihar Xinjiang

cri

Yanzu lokacin hunturu ya yi a nan kasar Sin. Shi ya sa yin wasa da dusar kankara ya zama irin wani wasa ne da ke samun karbuwa sosai. Shiyyar Kanasi da ke arewacin jihar kabilar Uygur ta Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin wata shahararriyar shiyyar yawon shakatawa ce a nan kasar Sin, wadda take mallakar tabkin Kanasi da aka mayar da shi tamkar tabki mafi kyan gani a duniya da kuma sauran ni'imtattun wuraren da ke nuna kyan ganinsu na musamman da kuma wuraren da ke shafar al'adun mutane.

A sakamakon kasancewarta a tudu mai yanayin sanyi, yawan danshi ya yi daidai sosai a lokacin zafi tare da iska mai ni'ima a shiyyar Kanasi, shi ya sa dimbin masu yawon shakatawa kan zo shiyyar domin gudun zafi a lokacin zafi. Amma lokacin hunturu yana da tsayi sosai a nan, haka kuma yawan zafi mafi kankanta ya kai kusan digiri sentigrade 40 a kasa da sifiri. Shi ya sa tun daga karshen kwanaki 10 na ko wane watan Oktoba zuwa karshen ko wane watan Maris mai kamawa, babbar dusar kankara kan mamaye manyan duwatsu, ta kan toshe hanyoyi kwata kwata, ba a iya yin bulaguro a shiyyar a lokacin hunturu. Duk da haka abin farin ciki shi ne yanzu an kyautata irin wannan hali. Yau ma bari mu yi hira da matafiya a rukuni na farko da suka yi bulaguro a shiyyar Kanasi a lokacin hunturu domin mu ji farin ciki da suka yi a sakamakon kallon dusar kankara.

A ran 2 ga watan Janairu na wannan shekara, masu sha'awar daukar hoto da kuma matafiya fiye da 500 a gida da wajen kasar Sin sun zo shiyyar Kanasi cikin motoci fiye da 100 domin halartar shagalin daukar hoto kan dusar kankara a shiyyar Kanasi. A karo na farko ke nan da matafiya suka iya yin yawo a wannan shiyya cikin mota a lokacin hunturu, shi ya sa suka yi matukar farin ciki.

Burin yin yawon shakatawa a shiyyar Kanasi a lokacin hunturu ya cika ne a sakamakon makudan kudaden da aka zuba kan wannan shiyya. A gabannin lokacin hunturu na shekarar bara, an yi amfani da kudin Sin yuan miliyan 3 domin sayen injuna na kawar da dusar kankara da kankara a kan hanya a shiyyar Kanasi domin tabbatar da rashin toshewar hanyoyi a shiyya. Ta haka matafiya sun iya shiga shiyyar kai tsaye cikin mota.

Zhou Lei, wadda ke sha'awar daukar hoto ta taba shiga shiyyar Kanasi kan keken musamman da doki ya ja. Amma a wannan karo, ta iya shiga shiyyar cikin mota. Ta gaya mana cewa,"A karon da ya gabata, na yi kwanaki 4 a kan hanyata ta kaiwa da kawowa tare da yin zango a babban dutse har na tsawon kwanaki 2. A cikin dare ana sanyi sosai da sosai, har ma injin auna yawan zafi da wani mutum ke mallaka ba ya iya aiki sosai. A kan hanyata, na ji kamar yatsun hannuna sun fadi a kasa a sakamakon daskarewa. Na sha wahala sosai. Amma a bana, an sami kyautatuwa sosai a nan. Cikin 'yan awoyi na samu isa kololuwar babban dutsen."

1 2 3