
Wani abu daban da ya jawo hankulan mutane shi ne, a gun wannan taro kuma za a bayar da wani rahoto mai fadi a ji kuma mai sunan "Rahoton bunkasa albarkatun ruwa na duniya" na MDD wanda akan bayar sau daya a kowadanne shekaru 3.
Bisa matsayinta na wata kasa mai tasowa kuma mafi girma na duniya, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan wannan taron. Ministan tsare ruwa na kasar Sin Chen Lei zai shugabanci tawagar gwamnatin kasar wadda take hade da jami'an ma'aikatar tsare ruwa da ta harkokin waje da ta noma da kuma hukumar yanayin zama ta kasar Sin don halartar taron matakin minista da sauran tarurrukan da abin ya shafa. Minista Chen Lei zai yi muhimmin jawabi a gun taron dandalin ruwa kuma bisa sunan gwamnatin kasar Sin, ban da wannan kuma zai yi shawarwari a tsakaninsa da jami'ain sassan kula da ayyukan tsare ruwa na kasar Japan da na Korea ta kudu da na hukumar ruwa ta duniya da na kungiyoyin kasa da kasa. (Umaru) 1 2 3
|