Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-17 15:20:00    
An bude taron dandalin ruwa a karo na 5 da nunin harkokin ruwa na duniya a birnin Istanbul

cri

A ranar da aka bude taron, an yi wani taron koli wanda ya zama taron da aka yi a karo na farko a tarihi a tsakanin shugannin kasashe da na gwamnatoci kan batun albarkatun ruwa, sabo da haka taron ya janyo hankulan mutane sosai. Shugabannin kasashe da na kungiyoyin kasa da kasa 13 ciki har da shugaban kasar Turkey Abdullah Gul da shugaban kasar Iraqi Jalal al-Tlabani da mataimakin babban sakataren MDD Sha Zukang sun halarci taron. Shugaba Abdullah Gul na kasar Turkey ya jaddada  a gun bikin bude taron cewa, aikin da ake yi domin daidaita matsalar karacin ruwa, ba ma kawai yana bukatar samun goyon baya daga fannin fasaha ba, abu mai muhimmanci kuma shi ne yana bukatar samun kulawa daga fannin siyasa. Yaya za a kiyaye albarkatun ruwa? Wani babban kalubalen da ke cin tuwo a kwarya ga dukkan kasashe da shiyyoyin duniya, wanda ba ma kawai ya shafi zaman al'umma ba, kuma yana jibintar tattalin arziki.

Bisa shirin da aka tsayar an ce za a yi wani muhimmin aiki daban wato za a kira wani taron matakin minista a karshen wannan taron dandalin ruwa. A lokacin kuwa da akwai ministocin tsare ruwa da kiyaye muhalli da sauran jami'ai takwaransu wadanda suka zo daga kasashe da shiyyoyi fiye da 100 za su halarci taron, inda za su yi musanyar fasahar tsare ruwa tsakanin kasashe daban-daban da bayyana wa junansu nasarorin da suka samu daga wannan fanni, kuma za su yi shawarwari a tsakaninsu kan matsalar kyautata albarkatun ruwa.

1 2 3