|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2009-03-17 15:20:00
|
 |
An bude taron dandalin ruwa a karo na 5 da nunin harkokin ruwa na duniya a birnin Istanbul
cri
 A ran 16 ga wata an bude taron dandalin ruwa na duniya a karo na 5 wanda aka shefe kwanaki 7 ana yin sa a birnin Istanbul, babban birni na farko na kasar Turkey, wanda kuma da akwai wakilai fiye da dubu 20 wadanda suka zo daga kasashe da shiyyoyi fiye da 100 ciki har da kasar Sin da kungiyoyin kasashen duniya 13 suka halarta. Babban jigon wannan taro shi ne "Hau da gadar daidaita matsalar albarkatun ruwa", makasudin taron kuma shi ne kara yin tuntuba da mu'amala tsakanin kasa da kasa domin gudanar da harkokin ruwa da kyau da daidaita rikici a tsakaninsu kan batun albarkatun ruwa.
Hukumar kular da harkokin ruwa ta duniya ita ce ta shirya wannan taron dandalin albarkatun ruwa na duniya, taron kuma ya kasance harkokin kasa da kasa mafi girma a fannin albarkatun ruwa. A shekarar 1997, hukumar ruwa ta duniya ta shirya taron kasa da kasa mafi girma a fannin albarkatun ruwa a wani birnin da ke kasar Morocco. Daga baya kuma akan yi taron sau daya a kowadanne shekaru 3.
1 2 3
|
|
|