Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-16 21:51:45    
Kasar Sin da kasar Aljeriya suna hada kan juna sosai a fannin tattalin arziki

cri

Madam Xie ta nuna cewa, kwangilolin ayyukan yau da kullum da kasar Sin ta samu a kasar Aljeriya sun fi muhimmanci lokacin da ake hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu. A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, irin wannan hadin gwiwa ta samu cigaba cikin sauri sosai. Musamman manyan kamfanonin kasar Sin sun fi bayar da gudummawa a kan irin wannan hadin gwiwa. Madam Xie ta ce, "Ya zuwa yanzu, yawan kamfanoni da masana'antun da kasar Sin ta zuba jari kuma ta kafa a kasar Aljeriya ya riga ya kai fiye da 30. Manyan kamfanoni, kamar su kamfanin gine-gine na kasar Sin da kamfanin CCECC da ChinaPetrol da ChinaPetrolChemy da kamfanin shimfida hanyar dogo ta kasar Sin sun bayar da gudummawarsu wajen ba da jagoranci. A karkashin tasirinsu, kamfanonin wurare daban daban na kasar Sin sun kuma tafi kasar Aljeriya domin neman kwangilolin ayyukan yau da kullum. Sakamakon haka, 'yan kwadago Sinawa masu dimbin yawa sun kuma samu aikin yi a kasar Aljeriya. Yanzu yawan 'yan kwadago Sinawa da suke aiki a Aljeriya ya kai kimanin dubu 30."

A cikin ayyukan yau da kullum da ake yi a kasar Aljeriya, wani aikin da ya fi jawo hankalin mutane shi ne tagwayen hanyoyin mota da ke hada gabas da yammacin kasar Aljeriya. Wannan aiki ne mafi girma a cikin tarihin kasar Aljeriya. A watan Agusta na shekara ta 2008, kamfanin Zhong Xin na kasar Sin da kamfanin shimfida hanyar dogo ta kasar Sin sun samu kwangilar shimfida wasu sassa na wannan tagwayen hanyar mota cikin hadin gwiwa. Jimillar tsawon sassan wannan tagwayen hanyar mota da kamfanonin kasar Sin suka samu ya kai kilomita 528, yawan kudin kwangila ya kai dalar Amurka biliyan 6.25.

Lokacin da Hua Dongyi, babban direktan ofishin kula da aikin cika kwangilar gina wannan tagwayen hanyar mota a kasar Aljeriya ya gaya wa wakilinmu cewa, yanzu ana gina wannan tagwayen hanyar mota bisa shirin da aka tsara. Mr. Hua ya ce, "Yanzu kasashen Afirka da yawa suna mai da hankali kan wadannan ayyukan da muke yi sabo da wadannan tagwayen hanyoyi ne da suka ratsa yankunan Magreb, wato suna shafar kasashen Morocco da Tunisiya da Libya. A 'yan kwanakin nan, lokacin da muke neman kwangiloli a sauran kasashen yammacin Afirka, kasashe da yawa sun zo kasar Aljeriya sun tambayi mai mallakar wannan tagwayen hanyar mota na kasar Aljeriya game da aikin da muke yi. Sabo da haka, a gun kamfaninmu, wadannan tagwayen hanyoyin mota suna kasancewa tamkar wani kati na kamfanoni masu jarin kasar Sin a Afirka." (Sanusi Chen)


1 2 3