Bayan da aka kafa huldar diplomasiyya a tsanake a tsakanin kasar Sin da kasar Aljeriya a ran 20 ga watan Disamba na shekara ta 1958, wato yau da shekaru 50 da suka gabata, a watan Satumba na shekarar 1964, an daddale yarjejeniyar farko a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu, sannan a watan Mayu na shekarar 1979 da watan Oktoba na shekarar 1999, an sake kulla sabbin yarjejeniyoyin raya cinikayya a tsakanin kasashen biyu. Haka kuma, a watan Oktoba na shekarar 1996, an kulla yarjejeniyar kare jarin da ake zubawa a tsakanin kasashen biyu. Bugu da kari kuma a watan Nuwamba na shekara ta 2006, an kulla yarjejeniyar magance buga haraji sau biyu a tsakanin kasashen biyu.
Lokacin da take zantawa kan yadda ake hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu, madam Xie Zhongmei wadda ke kula da hadin gwiwar tattalin arziki a sashen yankunan yammacin Asiya da na Afirka na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta ce, "A shekara ta 2007, yawan kudaden cinikayya da aka yi a tsakanin kasashen Sin da Aljeriya ya kai dalar Amurka biliyan 3.83, wato ya karu da kashi 83 cikin kashi dari bisa na shekara ta 2006. A tsakanin watan Janairu da watan Yuli na shekara ta 2008, yawan kudaden cinikayya da aka yi a tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan 2.53, wato ya karu da kashi 32 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekara ta 2006. Muhimman kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasar Aljeriya daga kasar Sin su ne injunan lantarki da motoci da kayayyakin gyara da tufafi da kayayyakin ingantaccen karfe da dai makamatansu."
Xie Zhongmei ta kara da cewa, ya zuwa karshen watan Yuni na shekara ta 2008, jimillar jarin da kasar Sin ta zuba a kasar Aljeriya ya riga ya kai dalar Amurka miliyan 640. An zuba galibin jari a fannin man fetur. A waje daya, yawan kudaden da kasar Aljeriya ta zuba a fannonin yin tufafi da kayayyakin karatu da na leda a kasar Sin ya kai dalar Amurka kimanin miliyan 22.
Ana kiran kasar Aljeriya "tankin man fetur na arewacin Afirka". Sabo da haka, kasar Aljeriya muhimmiyar kasa ce a Afirka wajen samar da man fetur da man gas, kuma ita ce kasa ta biyu da ke cikin kasashe mafi girma a cikin membobin kungiyar OPEC wajen samar da man gas. A cikin dogon lokacin da ya wuce, masana'antun man fetur da na gas muhimman ginshiki ne ga tattalin arzikin kasar Aljeriya. Yawan kudaden da aka samu daga wajen masana'antun man fetur domin samar da kadarorin duk kasar ya kai kashi 30 cikin kashi dari, kuma yawan harajin da aka buga kan masan'antun man fetur ya kai kashi 60 cikin kashi dari daga dukkan kasafin kudi na kasar Aljeriya.
1 2 3
|