Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-16 21:51:45    
Kasar Sin da kasar Aljeriya suna hada kan juna sosai a fannin tattalin arziki

cri

A shekara ta 2000 da ta 2001, kamfanin China Petrol?Chemical da kamfanin China Petrol bi da bi sun shiga kasar Aljeriya domin raya kasuwar makamashi domin biyan bukatun da kasar Sin ke da su wajen raya tattalin arziki. Mr. Wang Youyong wanda ke nazarin batun makamashi a jami'ar koyon harsunan waje ta Shanghai yana ganin cewa, a bayyane kasashen Sin da Aljeriya za su iya taimakawa juna wajen yin hadin gwiwa a fannin makamashi. Ko da yake kasashen biyu sun makara wajen yin hadin gwiwa, amma yanzu sun riga sun samu sakamako sosai. Mr. Wang ya ce, "A matsayin wata kasa wadda ke shigar da man fetur, kasar Sin tana mai da hankali kan yadda za a shigar da makamashi lami lafiya. Ba ma kawai ana bukatar shigar da jarin waje domin kafa tsarin adana man fetur bisa manyan tsare tsare ba, hatta ma tana bukatar zuba jarinta a kasashen waje domin kafa sansanonin samar da man fetur a ketare. A waje daya kuma, a matsayin wata kasa wadda ke fitar da man fetur, kasar Aljeriya tana mai da hankali kan yadda za a fitar da man fetur kamar yadda ya kamata. Ba ma kawai tana zuba jari a masana'antun sarrafa man fetur a kasashen da ke shigar da man fetur daga Aljeriya ba, har ma tana bukatar shigar da jari domin tabbatar da kasuwa a ketare domin tabbatar da karfin samar da man fetur. Sabo da haka, kasashen biyu suna zuba jari ga juna ko suke zuba jari tare, wannan yana dacewa da babbar moriyar kasashen biyu, za su iya samun moriya da nasara tare. Sabo da haka, irin wannan hadin gwiwa yana da muhimmiyar ma'ana bisa manyan tsare-tsare."

Bugu da kari kuma, neman kwangiloli da yin hadin gwiwa a fannin samar da 'yan kwadago wani halin musamman ne ga hadin gwiwar da ake yi a tsakanin kasashen Sin da Aljeriya. Madam Xie Zhongmei ta kara da cewa, "An fara yin hadin gwiwa a fannin neman kwangilolin ayyuka na yau da kullum, kamar su shimfida hanyoyin mota da gina gidajen kwana da yin gine-ginen ofis da hanyoyin dogo da na sadarwa da dai makamantansu a tsakanin kasashen biyu tun daga shekarar 1980. Ya zuwa karshen watan Yuli na shekara ta 2008, yawan kudaden kwangilolin da bangaren kasar Sin ya samu a kasar Aljeriya ya riga ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 19. Bugu da kari kuma, yawan 'yan kwadago Sinawa da suke aiki a kasar Aljeriya ya kai kimanin dubu 30. Muhimman ayyukan da suke yi su ne, giggina wasu otel-otel da kulob na sansanin soja da filin saukar jiragen sama na Aljiers da dai sauransu. Sannan, yanzu suna shimfida tagwayen hanyoyin mota da ke hada gabashin kasar da na yamma da sabon ginin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Aljeriya da kuma shimfida bututun sufurin ruwa da gidan kurkuku na ma'aikatar shari'a ta kasar Aljeriya da makamatansu."

1 2 3