Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 19:06:26    
Dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ta cim ma burin kara ci gaba cikin lumana

cri

Yang Jiechi ya bayyana cewa, abun farin ciki gare mu shi ne, a cikin kwanaki 50 da sabuwar gwamnatin kasar Amurka ta hau kan kujerar mulki, bangarori biyu Sin da Amurka sun yi kokari tare, saboda haka sun cim ma burinsu na kara dankon huldar da ke tsakaninsu cikin lumana.Yang Jiechi ya bayyana cewa, Manyan shugabanni da sassa daban daban na kasashen biyu sun riga sun kafa huldar aiki mai kyau a tsakaninsu. Shugaba Hu Jintao da shugaba Obama sun riga sun buga wa juna wayar telephoon, inda suka sami ra'ayi daya mai muhimmanci sosai a kan raya huldar da ke tsakanin kasashen biyu a sabon zamani. Sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton ta sami nasara wajen kai wa kasar Sin ziyara, wannan ya kara wa bangarorin biyu fahimta da yin hadin guiwa a tsakaninsu. Kasashen biyu suna ci gaba da yin cudanya da daidaituwa sosai a tsakaninsu biyu da bangarori da yawa, wannan sabon masomin da aka samu ya kafa tushen raya dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a sabon zamani .

Ranar 12 ga wata, Yangjiechi ya ba da lacca a birnin Washinton, inda ya bayyana cewa, yana fatan tsara fasalin makomar huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka tare da bangaren Amurka. Ya ce, shugaba Hu Jintao da shugaba Obama za su yi ganawar juna a lokacin taron koli kan harkokin kudi da za yi a birnin London bayan rabin watan. Ya ce, Wannan karo na farko ne da shugabannin kasashen biyu za su gana wa juna bayan da sabuwar gwamnatin kasar Amurka ta hau kan kujerar mulki, bangarorin biyu dukkansu suna mai da hankali a kai. Na yi imani sosai cewa, bisa kokarin da bangarorin biyu za su yi, tabbas ne za sa sami nasara a gun ganawar da za a yi. Yang Jiechi ya ci gaba da bayyana cewa, A halin yanzu, aiki mai muhimmanci da za a yi shi ne kara karfafa hadin guiwa don shawo kan rikicin kudi na kasa da kasa da kuma kiyaye da zaunar da harkokin kudi da tattalin arziki cikin hadin guiwa. Tun daga ranar haifar da rikicin kudi har zuwa yanzu, kasar Sin da kasar Amurka suna yin cudanya da daidaitawa a tsakaninsu sosai tare da samun sakamako, wannan ya ba da muhimmin taimako na sa kaimi ga shawo kan rikicin kudi cikin hadin guiwa a tsakanin kasa da kasa.

1 2 3