Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 19:06:26    
Dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ta cim ma burin kara ci gaba cikin lumana

cri

Yanzu, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi yana ziyarar aiki a kasar Amurka. A ranar 12 ga wannan wata, Yang Jiechi ya yi jawabi a gun aikace-aikacen maraba da shi da cibiyar yin nazari kan manyan tsare-tsare da batutuwan kasa da kasa ta kasar Amurka da kwamitin kula da harkokin cinikayya tsakanin Sin da Amurka suka shirya cikin hadin guiwa, inda ya bayyana cewa, tun daga sabuwar gwamnatin kasar Amurka ta hau kan kujerar mulkin kasa har zuwa yanzu, bangarori biyu Sin da Amurka sun cim ma burinsu na kara samun ci gaba wajen dangantakar da ke tsakaninsu. Ya ce, huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ta sami sabuwar damar tarihi wajen bunkasuwa, ya kamata kasashen biyu su kara daga huldar da ke tsakaninsu zuwa sabon matsayin hadin guiwa a dukkan fannoni.

A ranar 9 ga wannan wata, Yang Jiechi ya soma ziyararsa ta aiki cikin kwanaki biyar a kasar Amurka bisa gayyatar da sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka Hillary Clinton ta yi masa. A duk tsawon lokacin ziyararsa, bi da bi ne ya yi shawarwari da Hillary da ministan kudi Timothy Geithner da mai ba da shawarwari ga harkokin tsaron kasa Jemes Jones da shugaba Obama da mataimakin shugaba Joe Biden da wakilin musamman na harkokin Aghanistan da Pakistan Richard Holbrooke. Bangarorin biyu sun musanya ra'ayoyinsu sosai a kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya shiyya da suka jawo hankulansu dukka, kuma sun sami ra'ayi daya a fannoni da yawa.

1 2 3