Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-12 13:48:58    
Wani gwanin Sin ya karyata zargin da bangaren kasar Amurka ya ya yi na cewar wai jiragen ruwan yakin Sin sun yi muzgunawa ga jirgin ruwan Amurka

cri

To, daga cikin wannan sanarwa da hukumar mulkin kasar Amurka ta bayar, ana iya ganin cewa jirgin ruwan da bangaren Amurka ya rada masa sunan ' USS Impeccabal' wani jirgin ruwa ne dake yin aikin nazari. Amma, farfesa Meng Xiangqing daga kolejin nazarin dangantakar kasa da kasa ta Jami'ar koyon ilmin tsaro ta kasar Sin ya bayyana ra'ayinsa cewa : 'Tashar internet ta sojojin ruwan Amurka ta yi bayani a fili cewa jirgin ruwa mai suna USS Impeccable yana daga daga cikin jiragen ruwa guda biyar na sojojin ruwan Amurka, wanda musamman ne ya kan bada taimako ga ayyukan ofishin tsaron gida da ake kira The Pen-tagon a Turance da kuma sauran hukumomin gwamnatin kasar Amurka ; Ban da wannan kuma, kafofin yada labarai na kasar Amurka su ma sun taba bayar da labarin cewa a matsayin wani jirgin ruwan leken asiri mallakar sojojin ruwan kasar Amurka, jirgin ruwa mai suna USS Impeccable ya kasance sirri ne da kowa ya sani. Saboda haka, ana iya tabbatar da cewa, wannan jirgin ruwan soji ne na musamman'.

Jama'a masu sauraro, abin da muke so mu gaya muku shi ne, bangaren kasar Amurka ya sha jaddada cewa wai jirgin ruwa mai suna ' USS Impeccable' ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata a yankin ruwan teken kasa da kasa. Amma, a zahiri dai, wurin da yake zamewa na da nisan kilomita 120 kawai daga tsibirin Hainan na kasar Sin. Ko shakka babu, wannan wuri shi ne yankin musamman na tattalin arziki na kasar Sin. Game da wannan dai, Farfesa Meng Xiangqing ya furta cewa 'Wani jirgin ruwan yaki mai leken asiri na sojojin kasar Amurka ya zo nan yankin ruwa na musamman na tattalin arzikin kasar Sin ba tare da samun izininta ba. Lallai ya karya wasu jeren dokokin shari'a na MDD da kuma na kasar Sin'.

1 2 3