Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, a jiya Larawa, kakakin ma'aikatar harkokokin wajen kasar Sin, Ma Zhaoxu ya sake karyata zargin da kasar Amurka ta yi na cewar wai jiragen ruwan kasar Sin sun yi muzgunawa ga jirgin ruwan sa ido na kasar Amurka. Mr. Ma ya ce kalamin bangaren Amurka ya kauce wa hakikanin abubuwa. Saboda haka, bangaren kasar Sin ya yi watsi da haka. To, mene ne ainihin halin lamarin ? Jirgin ruwan sa ido mai suna ' USS Impeccable', wane irin jirgi ne ? kuma wane irin halin zuciya ne da bangaren kasar Amurka yake da shi sanda yake yin tashin hankali ?
An labarta cewa, fadar White House ta Amurka da majalisar gudanarwa da kuma ma'aikatar tsaron kasar Amurka ko wanensu ya bayar da sanarwa a ranar 9 ga wata, inda suka yi ikirarin cewa wai jiragen ruwa guda biyar na kasar Sin sun yi muzgunawa ga wani jirgin ruwan yaki na kasar Amurka mai suna ' USS Impeccable' yayin da yake yin awo a karkashin ruwa dake kudancin tekun kasar Sin a ranar 8 ga wata ; sa'annan sun ce bangaren Amurka ya rigaya ya kai kara ga bangaren Sin kan lamarin.
1 2 3
|