Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-18 15:54:29    
Wurin tarihi na Sanxingdui mai ban mamaki

cri

Saboda wurin tarihi na Sanxingdui ya bar mutane cikin dubu sosai, shi ya sa a cikin shekaru fiye da 10 bayan da aka bude kofar dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na Sanxingdui, mutane da yawa da ba a iya kidaya yawansu ba sun kawo wa wannan dakin nune-nune ziyara. Zhang Jizhong, mataimakin shugaban wannan dakin nune-nune ya bayyana cewa, kayayyakin gargajiya masu ban mamaki da kuma wayewar kai mai dogon tarihi kuma mai daure kai na wurin tarihi na Sanxingdui sun jawo hankulan masu yawon shakatawa na kasashen waje kwarai da gaske. Ya kara da cewa:

"Abun da ya fi jawo sha'awar matafiya su ne al'adu mai dogon tarihi da kuma ban mamaki da aka samu a wurin tarihi na Sanxingdui. A kasashen waje, al'adun Sanxingdui sun yi fice sosai a cikin wayewar kai da aka samu a yankunan kogin Yangtse. Kayayyakin tarihi da aka samu a wurin tarihi na Sanxingdui na da kyau sosai, kuma ba a samu irinsu a sauran sassan duniya ba, sun nuna halayen musamman na al'adun kasashen gabashin duniya da kuma na lardin Sichuan sosai. Matafiya baki sun nuna sha'awa sosai kan wadannan kayayyakin tarihi."

Madam Sirkka Korela, 'yar kasar Finland, tana daya daga cikin dimbin matafiya da suka zo daga kasashen ketare. Ta nuna mamaki ga wurin tarihi na Sanxingdui kwarai. Ta ce:

"An ajiye kayayyakin gargajiya ta hanya mai cikakken bambanci. Abubuwan da suka fi jawo hankalina su ne wadannan kayayyakin tarihi, musamman ma abubuwan rufe fuska masu ban mamaki, haka kuma wadannan itatuwan tagulla da tsuntsayen da aka yi da tagulla."

To, masu sauraro, kafin mu sa aya ga shirinmu na yau, bari mu maimaita tambayoyi 2 da muka yi muku. Da farko shekaru nawa ne yanzu da wurin tarihi na Sanxingdui ya yi suna sosai? Na biyu kuma, a cikin abubuwan tarihi da aka tono daga karkashin wurin tarihi na Sanxingdui, mene ne ya fi nuna nagartacciyar fasahar zamanin da, abubuwan da aka yi da lu'ulu'u ko kuma wadanda aka yi da tagulla?


1 2 3