Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-18 15:54:29    
Wurin tarihi na Sanxingdui mai ban mamaki

cri

A cikin shirinmu na yau, za mu kai ziyara ga wani wurin tarihi mai suna Sanxingdui. Kafin mu soma shirinmu na yau, bari mu fara da yi muku tambayoyi 2 tukuna. Da farko, yau da shekaru nawa ke nan da wurin tarihi na Sanxingdui ya yi suna sosai? Na biyu kuma, a cikin abubuwan tarihi da aka tono daga karkashin kasar wurin tarihi na Sanxingdui, mene ne ya fi nuna nagartacciyar fasahar zamanin da, abubuwan da aka yi da lu'ulu'u ko kuma wadanda aka yi da tagulla?

Babu wanda zai iya kiyasta cewa, ayyukan da wani bakauye na kauyen Sanxing ya yi a gonakinsa a lokacin bazara sun haifar da gano wani abu mai ban mamaki. Ganowar da aka yi ta wabbab abu ba zato da kuma hakar kayayyakin gargajiya da nazarin da aka yi shekaru gomai ana yi sun tabbatar da cewa, yau da shekaru dubu 5 zuwa dubu 3 da suka wuce, kauyen Sanxing babban birnin ne na karamar kasar Shu ta zamanin da, wayewar kai da aka samu a wannan wuri ya taba yin hazaka har shekaru misalin dubu 2 da suka wuce. Saboda gano wurin tarihi na Sanxingdui, an tsawaita tarihin karamar kasar Shu da shekaru dubu 2. Saboda irin wannan muhimmiyar ganowa, an kyautata tsarin tarihin wayewar kai na kasar Sin, haka ya kuma nuna cewa, wayewar kai na Kogin Yangtze da wayewar kai na wurin tarihi na Sanxingdui yake wakilta ya yi daidai da na Rawayan Kogi, dukkansu suna cikin tsarin wayewar kai na kasar Sin.

Kauyen Sanxing yana cikin lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin. An gina dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya mai suna Sanxingdui a wurin tarihi na Sanxingdui yau da shekaru misalin 10 da suka wuce.

Madam Qiu Xueqing, wata mai ba da karin haske da ke aiki a wannan dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya ta bayyana cewa, ganowar wannan wurin tarihi na wayewar kai yana da muhimmanci sosai. Ta ce:

"An gano wannan wurin tarihi ne a kan layin da ya zagaye duniya a arewa mai misali digiri 30, ban da shi kuma, akwai babban dutse na Everest da wayewar kai na yankin Maya da babban tsibiri na Bermuda a kan wannan layi. Dukansu suna da ban mamaki. Wurin tarihi na Sanxingdui, wani birni ne na zamanin da, inda aka fi samun kayayyakin gargajiya, sa'an nan kuma, tarihinsa ya fi tsayi, kuma yana kunshe da abubuwan al'adu mafiya yawa a dukan yankin kudu maso yammacin kasar Sin har zuwa yanzu."

Masu ilmin nazarin kayayyakin gargajiya sun gano cewa, yau da shekaru misalin dubu 3 da suka wuce, an yi watsi da wannan cikakken birni ba zato ba tsammani, shi ya sa aka sa aya ga nagartaccen wayewar kai na Sanxingdui ba zato ba tsammani. Akwai jita-jita da yawa kan ainihin dalilin da ya sa aka yi watsi da wannan birni mai tsawon shekaru misalin dubu 2, amma har zuwa yanzu dai yana bai wa mutane mamaki sosai, saboda babu rubutu ta fuskar tarihi.


1 2 3