Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-18 15:54:29    
Wurin tarihi na Sanxingdui mai ban mamaki

cri

Kayayyakin gargajiya da aka samu a wurin tarihi na Sanxingdui sun fi ba mutane mamaki. Madam Qiu Xueqing ta gaya mana cewa, abubuwan da suka fi jawo hankali a wurin tarihi na Sanxingdui su ne kayayyakin da aka yi da tagulla. Sifofin wasu mutum-mutumin tagulla sun sha bamban da na mutanen kasashen Asiya kwarai, suna da manyan idanu da kuma hanci mai tsayi. Ta kuma yi mana karin bayani kan wani kayan tarihi da yake matsayin alamar dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na Sanxingdui, wato wani abin rufe fuska da aka yi da tagulla. Ta ce:

"Wannan shi ne abin rufe fuska mafi girma a duk duniya da aka yi da tagulla. Shi ne dukiyar kasarmu mai daraja. Ya sha bamban da saura sosai, musammam ma kamannin wannan abin rufe fuska."

Humbert Droz ya zo daga kasar Faransa, ya mai da hankali sosai kan wani kayan tarihi a wannan dakin nune-nune, wato wani icen tagulla. Wannan mai yin ziyara da ya zo kasar Sin daga Faransa mai nisa ya ce:

"Yau da shekaru da dama da suka wuce, an taba nuna wadannan kayayyakin tarihi a Faransa. Ko da yake na san kasar Sin tana da dogon tarihi, amma a lokacin da na sake ganin wadannan kayayyakin tarihi, na ji mamaki sosai kamar yadda na yi a da."

Wannan icen tagulla da ya jawo hankalin Mr Droz an mayar da shi tamkar abin al'ajabi na duniya. Tsayin rassansa ya kai misalin mita 3.6. A idon mutanen Sin na zamanin da, ice yana matsayin alamar sararin samaniya gaba daya, taurari da wata da rana da duniya dukkansu sun yi kama da 'ya'ya ne da ke kan icen. Madam Qiu ta yi mana bayani kan wannan ice:

"Wannan icen tagulla, kayan tagulla ne mafi kyau, da aka jure wahala sosai wajen kera shi, kuma an kera shi ne a tsanake. Ba a iya ganin irin wannan siffar icen tagulla a sauran sassan duniya, kuma ba a taba samun fasahar kerawa kamar haka ba. An kera wannan babban icen tagulla bisa matakai. Mun gano itatuwan tagulla 8 a wurin, amma guda 2 daga cikinsu kawai muka iya gyara su kwata kwata. An yi shekaru 3 ana gyara daya daga cikinsu."

A hakika kuma, ban da nagartacciyar fasaha, wadannan itatuwan tagulla sun bayyana ra'ayin da mutanen kasar Sin suka tsaya a kai a kan lamarin duniya a zamanin da.

Ma iya cewa, kayayyakin tagulla sun fi wakiltar kayayyakin gargajiya da aka samu a wurin tarihi na Sanxingdui. Sun fi nuna nagartacciyar fasaha ta wancan lokaci.


1 2 3