Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-18 09:51:46    
Kasuwar motoci ta Beijing bayan da aka daidaita harajin da ake buga wa motoci

cri

Dimbin mutane wadanda suke da shirin sayen motoci sun amince da ra'ayin Mr. Liu. Yanzu farashin man fetur yana ta karuwa, mutane masu rayuwa gwargwadon hali yanzu sun fi mai da hankali kan motoci masu kananan injuna.

Gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da manufar rage harajin da ake bugawa kan motoci masu kananan injuna, hakan wata kyakkyawar dama ce ga masana'antun kasar Sin wadanda suke samar da motoci da ke da samfurorinsu. Yanzu kusan dukkan masana'antun kera motoci na kasar Sin suna samar da motoci masu kananan injuna. Malama Hui Yumei wadda ta dade tana nazarin sana'ar mota ta kasar Sin ta gaya wa wakilinmu cewa, "A cikin motoci masu kananan injuna kuma masu arha, masana'antunmu ne suke kera kusan dukkansu. Idan an iya yin tsimin daruruwan yuan ga kowace mota, za a iya yin amfani da wadannan kudade domin nazarin sabbin salonsu da kuma kyautata ingancinsu. Sakamakon haka, kasuwar motocin samfurorin kasarmu za ta iya samun cigaba yadda ya kamata. Kuma za a iya sa kaimi kan masana'antun da ke kera motoci masu kananan injuna."

Masana'antun kera motoci masu kananan injuna na kasar Sin sun amince da ra'ayin madam Hui Yumei. Mr. Shang Yugui wanda ke kula da aikin yada alamar mota kirar Great Wall ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Tabbas ne a nan gaba, kamfaninmu zai kara samar da motoci masu kananan injuna. Alal misali, a watan Nuwamba na shekarar da muke ciki, za mu samar da wani sabon salon mota mai lita 1.3 a kasuwa. Sannan a watan Mayu na shekara mai zuwa, za mu samar da wata mota mai lita 1.5 kawai a kasuwa."

Bugu da kari kuma, kusan dukkan mutanen da suka yi hira tare da wakilinmu sun bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da wannan manufar daidaita harajin mota, wannan ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta sa niyya sosai wajen raya wata al'umma mai tsimin makamashi da kiyaye muhalli. Sun yi tsammani cewa, a cikin halin hauhawar farashin man fetur da ake ciki yanzu, idan gwamnatin kasar Sin ta kara bayar da manufofin tallafawa motoci masu kananan injuna, tabbas ne kasuwar motoci masu kananan injuna tana da haske sosai. (Sanusi Chen)


1 2 3