Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-18 09:51:46    
Kasuwar motoci ta Beijing bayan da aka daidaita harajin da ake buga wa motoci

cri

Tun daga ran 1 ga watan Satumba na shekarar da muke ciki, kasar Sin ta daidaita harajin da take bugawa kan motocin da ake saye, wato ta soma buga karin haraji kan motoci masu manyan injuna, a waje daya, ta soma rage yawan harajin da take bugawa kan motoci masu kananan injuna. Ya zuwa yanzu, an riga an yi fiye da wata biyu ana aiwatar da wannan manufa. Yaya wannan manufa take yin tasiri ga kasuwar motoci? Yanzu ga wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana.

Kasuwar cinikin motoci da ke unguwar gasar Asiad ta Beijing kasuwar motoci ce mafi muhimmanci da ke bayyana yadda ake cinikin motoci a nan Beijing. Yawan motoci masu manyan injuna da aka shigo da su daga kasashen waje kuma ake sayar da su a wannan kasuwa ya kai kashi 1 cikin kashi biyar bisa na dukkan motoci masu manyan injuna da ake sayarwa a duk kasar Sin. Sabo da haka, wannan kasuwa ta yi daidai ta bayyana yadda wannan manufar daidaita harajin motoci take aiki. Lokacin da wakilinmu yake ziyara a wannan kasuwa, ya gano cewa, bayan da aka buga karin haraji kan motoci masu manyan injuna, farashinsu, kamar na BMW da Audi da Mercedez-Benz ya karu da kudin Sin tun daga yuan dubban gomai zuwa dubun daruruwa. Alal misali, yanzu farashin mota kirar BMWX5 ya hau daga kudin Sin yuan dubu 890 zuwa kimanin yuan miliyan 1 da dubu dari 1.

Lokacin da farashin irin wadannan motoci masu manyan injuna yake karuwa sosai, yawansu da ake sayarwa yana raguwa cikin sauri. Ko da yake yawan mutanen da su kan wannan kasuwa na da yawa, amma wadanda suka sa niyyar sa hannu kan kwangilar sayen irin wadannan motoci masu manyan injuna kadan ne. Mr. Su Hui, babban direktan kasuwar cinikin motoci da ke unguwar gasar Asiad ta Beijing ya bayyana cewa, "A watan Satumba, yawan motocin da aka sayar ba su cimma shirin da aka tsara ba. Wannan hakikanin abu ne da yake kasancewa a gabanmu. Ko da yake ana zuwa kasuwarmu sosai, amma ba kamar a watan Satumba da watan Oktoba na shekarar da ta gabata ba an sayar da motoci masu yawan gaske. Yawan motoci masu manyan injuna da aka sayar a watan Satumba na shekarar da muke ciki ya ragu sosai sakamakon wannan manufar daidaita harajin motoci. Alal misali yawan motoci masu fiye da lita 3 da aka sayar ya ragu fiye da kashi gomai bisa kashi dari, ba ya nufin ya ragu sosai. A bayyane yake, wannan manufa tana da amfanin kayyade yawan motoci masu manyan injuna da ake sayarwa."

Amma a hakika dai, ba ma kawai wannan manufar daidaita harajin motoci ta yi tasiri ga kasuwar motoci ba, har ma dalilai iri iri, kamar su a watan Agusta, wato kafin a soma aiwatar da wannan manufa, an sayi dimbin irin wadannan motoci masu manyan injuna cikin sauri kafin lokacin da suka tsara, kuma yanzu kasar Sin tana daidaita tattalin arzikinta daga dukkan fannoni, da kuma matsalar hada-hadar kudi da ta auku a duk duniya tare da hauhawar farashin man fetur cikin sauri, dukkansu suna yin tasiri ga kasuwar motoci masu manyan injuna.

Amma, sabo da wadanda suke sayen motoci masu manyan injuna suna da halin musamman, kuma suna da karfin yin amfani da irin wadannan motoci. Wannan ya tabbatar da cewa, ko da yake yanzu kasuwar motoci masu manyan injuna tana cikin lokacin lafawa. Kuma gwamnatin kasar Sin ta kara yawan haraji sosai kan motoci masu manyan injuna sabo da tana fatan za a rage yawan motoci masu manyan injuna da ake sayarwa, amma bisa binciken da aka yi a kasuwa, an gano cewa, wadanda suke son sayen irin wadannan motoci masu manyan injuna ba su mai da hankali kan farashinsu sosai ba.


1 2 3