Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-18 09:51:46    
Kasuwar motoci ta Beijing bayan da aka daidaita harajin da ake buga wa motoci

cri

Mr. Yang Cheng wanda ke tafiyar da wani kamfani mai zaman kansa, ya fi sha'awar motoci masu manyan injuna, kamar jeep. A cikin wadannan kwanakin da ake ciki, yana da shirin canja wata mota. Amma bai san sauyin manufar daidaita harajin motocin da ake saye ba. Ya gaya wa wakilinmu cewa, "Farashin motar da nake sha'awa ya kan kai kimanin kudin Sin yuan dubu dari 5. Wato, ko da yake an canja manufar daidaita yawan harajin motocin da ake saye, farashinsu ya karu da kudin Sin yuan dubu gomai, wannan ba damuwa. A wajenmu, abin da ya fi muhimmanci shi ne siffar mota, wato dole ne siffarsu tana da kyaun gani sabo da na kan halarci wasu muhimman bukukuwa. Sabo da haka, a ganina, irin wannan manufa ba za ta yi tasiri sosai ga masu arziki ba."

Mr. Su Hui, babban direktan kasuwar cinikin motoci da ke unguwar gasar Asiad ta Beijing ya kuma bayyana cewa, ba za a iya tsawaita lokacin lafawa da kasuwar cinikin motoci masu manyan injuna ke ciki ba. Bayan da aka daidaita farashin motoci masu manyan injuna, tabbas ne kasuwar motoci masu manyan injuna za ta koma hali kamar yadda ake ciki kafin a aiwatar da wannan manufa. Sabo da ko shakka babu ana bukatar motoci masu manyan injuna a kasuwa.

Bayan da aka aiwatar da manufar, ya kamata wadanda ke samar da motoci masu kananan injuna su fi samun moriya. Wakilinmu ya sadu da masu sayayya da yawa a kasuwa. Galibinsu sun bayyana cewa, wannan manufa ta yi tasiri sosai ga shirinsu na sayen mota. Wasu wadanda suke da shirin sayen motoci masu manyan injuna a da, yanzu sun canja shirinsu kuma sun soma zura idonsu kan motoci masu kananan injuna. Amma a waje daya, wasu daga cikinsu suna fatan ban da raguwar yawan harajin da ake bugawa kan motoci masu kananan injuna, gwamnati za ta iya samar da karin manufofin tallafawa motoci masu kananan injuna. Sabo da haka, motoci masu kananan injuna za su iya kara jawo hankalin mutane. Mr. Liu Zhi yana aiki a wata kafar yada labaru. Sabo da akwai nisa sosai a tsakanin gidansa da ofishinsa, yana son sayen wata mota. Ya ce, ya san manufar daidaita harajin motoci da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa, amma ya ce, wannan ba ainihin dalilin da ya sa ya tsai da kudurin sayen wata mota mai karamin inji ba ne. Ya ce, "Ina son sayen mota yanzu ba domin wannan manufa ba sabo da bisa wannan manufar, zan iya tsimin kudin Sin yuan daruruwa ne kadai. Abin da na fi mai da hankali shi ne yawan kudin da zan kashe lokacin da nake amfani da ita. Alal misali, ina fatan za a iya rage yawan kudin ajiye motoci masu kananan injuna da harajin hanya da ake bugawa. Idan an rage daruruwan yuan kadai, ba za a iya samun tasiri ga wadanda suke son sayen mota ba."


1 2 3