'Da farko, mun shiga tsarin ba da magani ga manoma cikin hadin gwiwa a kauyukanta, wato duk wani tsohon da shekarunsa na haihuwa suka wuce 70, zai biya kudin dalar Amurka kamar 1.5 kawai a ko wace shekara, idan ya kamu da ciwo, zai samu kudin tallafi. Bayan haka kuma, mun shiga tsarin tabbatar da mafi karancin jin dadin rayuwar jama'a. Gaskiya ne, tsare tsaren biyu sun kawo alheri sosai ga manoma.'
Ba kawai ba za a nuna damuwa wajen ganin likita ba, har ma a shekarar da ta wuce, an samu wani abin farin ciki ne a iyalin tsoho Ma, wato karamin jikansa Ma Feng ya ci jarrabawar shiga jami'ar ilmin sanin ma'adinai ta kasar Sin bisa maki mai kyau.
Tun lokacin kuruciyarsa, Ma Feng yana da kwarewa sosai kan karatu. Nan da shekaru goma da suka wuce, ya tabbatar da sauye-sauyen da aka samu a garinsa, abin da ya fi damunsa shi ne, sauye-sauyen da aka samu a makarantarsu.
'A lokacin da na shiga firamare, akwai malamai uku kawai, da dalibai sama da 90 a makarantarmu. Yanzu, akwai malamai fiye da 20, da dalibai fiye da 400 a cikin wannan makaranta.'
Yanzu, makarantar firamare da Ma Feng ya taba karatu a can, ta riga ta samu karuwa sosai wajen ingancin malamai, da azuzuwa. Bayan haka kuma, an kafa azuzuwan surkullen hanyoyin sadarwa, inda dalibai za su iya koyon fannonin ilimin labarin kasa, da Turanci ta hanyar kallon talabijin. Ban da wannan kuma, saboda gwamnatin wurin na fatan mayar da aikin ba da ilmi na birane da na kauyuka a matsayi daya, don haka, a kan aika da malamai masu inganci na makarantun firamare da ke birane zuwa makarantar da Ma Feng ya taba karatu a nan, don ba da ilmi.
Ma Feng ya taba karatu a makarantar sakandare ta Liu Panshan, wato makarantar sakandare da ta fi inganci a jihar Ningxia. A makarantar, ba kawai Ma Feng ya yi farin ciki sosai kan karatunsa ba, har ma ya samun taimako daga wajen manufofin samar da alheri a jere da aka kafa kan dalibai daga kananan kabilu, da kuma wuraren da ke kan tudu.
"A cikin makarantar sakandare ta Liu Panshan, ko wane dalibi na kauyuka na iya samun kudin zaman rayuwa na dalar Amurka kusan 11 a ko wane wata, kuma wadannan dalibai ba sa biyan kudin karatu, da na kwana, da na ruwa da wutar lantarki. Gaskiya ne mun samu alheri sosai daga manufofi a makarantar sakandare ta Liu Panshan."
Jami'ar ilmin sanin ma'adinai ta kasar Sin da Ma Feng ke karatu a yanzu tana birnin Wuhan da ke tsakiyar kasar Sin. Ga wadancan yaran da suka fito daga kauyuka, akwai abubuwa da yawa da ke birane da suke ba su mamaki da farin ciki. Amma, Ma Feng ya ce, kullum yana tunanin garinsa, da 'yan kabilarsu, da kuma iyalinsa, yana yin alfahari kan su. 1 2 3
|