A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani game da wani tsoho musulmi Ma Tingfu, da iyalinsa da ke zaune a jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui da ke yammacin kasar Sin. Shekarar da muke ciki, shekarar cikon shekaru 10 ce da iyalin tsoho Ma suka kaura zuwa sabon gida. A cikin shekarun goma, tsoho Ma, da iyalinsa sun yi kokari tare da 'yan uwansu da ke garinsu, don mayar da sararin hamada zaman gonaki, ta yadda suka yi zama mai dadi da wadata. Ko da ya ke suna zaune a kauye, amma kudin da suka samu sun da yawa bisa na wasu mutanen da ke zaune a manyan birane. A cikin shirinmu na yau kuma, bari mu ji labari game da tsoho Ma da iyalinsa.
Tsoho Ma, 'dan shekaru 74 na da 'ya'ya biyar da jikoki fiye da goma. Kuma wasu jikokinsa suna aikin jigila zuwa wurare daban daban, saboda haka, ba kawai su kan kawo 'ya'yan itace daga kudu, da kuma kayayyakin musamman daga sauran wurare ga kakanninsu ba, har ma su kan gaya musu sabbin lamuran da suka faru a wurare daban daban.
Ko da ya ke iyalin tsoho Ma na zaune a wani kauyen da ke da nisan kilomita 127 da birnin Yinchuan, babban hedkwatar jihar Ningxia, amma halin zaman rayuwarsu iri daya ne kamar na mutanen da ke birane. Tun fil azal, iyalin tsoho Ma suna zaune a wani wurin da ke kan tudu na jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui, a kan samu bala'in fari a can, saboda haka, mutanen da ke wurin suna shan wahalar rashin ruwa sosai, kuma suna fama da talauci. A shekaru goma da suka wuce, iyalin tsoho Ma sun yi kaura zuwa wannan yankin raya kasa mai suna Hong Si Bao. A lokacin ko da ya ke mutane kadan ne suke zaune a nan, amma an samu sauki wajen sufuri, kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne, aikin madatsar ruwa da kasar Sin ta yi a wurin da ke kusa da Hong Si Bao na iya shigar da ruwan da ke rayayen kogi don shayar da gonakai, haka kuma an warware matsalar rashin ruwa. Tsoho Ma Tingfu ya ce,
"Babu mutane da yawa da lokacin da muke yi kaura zuwa nan, amma daga baya kuma, an samar da ruwa, da wutar lantarki, har ma an yi gyare-gyaren hanyoyi, ta yadda muke iya aikin sufuri, bayan haka kuma, an gina makarantu, da masallaci. Gaskiya ne, mun samu sauki sosai."
1 2 3
|