Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-13 16:45:56    
Wani bayani game da wani tsoho musulmi Ma Tingfu

cri

Hong Si Bao, wani yankin raya kasa da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta zuba kudi da yawa don kafa shi don tsugunar da mutane, da ke fama da talauci. A cikin shekaru goma, manoma fiye da dubu 200 da suka taba zaman a wurare da ke fama da bala'in fari sun kaura zuwa wurin, inda 'yan kabilar Hui sun kai kashi 57 cikin dari. Yanzu, ana da kyakkyawan muhali a wurin. Ko da ya ke an gamu da bala'in fari mai tsanani a shekarar da ta wuce, amma an samu wadatar hatsi a nan. Ma Yingcheng, 'dan shekaru 50, wato karamin 'dan tsoho Ma ya ce,

"Gwamnatin kasarmu tana ta kara kudin tallafi wajen hatsi gare mu, kuma kullum tana bayar da kudi ga manoma don sayen takin zamani. A wurare masu fama da talauci kuma, a kan rarraba isassun kudade ga mutanen da ke bisa matsayin zaman rayuwa mafi kankanta. Lallai an samu sauye-sauyen zaman rayuwa sosai a garinmu."

A sakamakon hada aikin shuka, da aikin sufuri na zaman kansu, da kuma aikin fitar da 'yan kwadago, da dai sauransu da aka gudanar, a shekaru goma da suka wuce, yawan kudin da mutanen da ke Hong Si Bao suka samu ya karu da ninki biyar. Ma Chengying yana daya daga cikin wadanda suka samu karuwar kudi. Ya gina wani babban gida, kuma ya sayi motoci iri daban daban. Bayan haka kuma, ya taba bayar da kudi ga iyayensa don su je aikin hajji a Makka har sau biyu, ta yadda ya taimaka wajen cika fatan iyayensu.

Saboda ya damu da iyayensa za su kashe kudi da yawa kan ganin likita, Ma Yingcheng ya taba yin iyakacin kokari don samun kudi. A shekarar da ta wuce, mahaifiyarsa ta hadu da ciwon ciki, ba kawai ta samu jiyya kamar yadda ya kamata ba, kuma ba a kashe kudi da yawa ba, haka kuma Ma Chengying ba zai nuna damuwa kan wannan ba. Ya sheda wa wakilinmu cewa, a duk lokacin aikin jiyya, suna iya kashe kudi na dalar Amurka kusan 542, amma kudin tallafi daban daban da kasar Sin ta bayar sun kai kusan dalar Amurka 457, wato iyalinsa sun kashe kudi na dalar Amurka kamar 85 kawai. Tsoho Ma Tingfu ya ce, sun samu wadannan kudaden tallafi ne bisa sabon tsarin ba da magani ga manoma cikin hadin gwiwa a kauyukanta, da kuma tsarin tabbatar da mafi karancin jin dadin rayuwar jama'a da kasar Sin ke gudanarwa.


1 2 3