Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-13 16:41:45    
Labarai na game da wani tsoho

cri

Liu Dan ta gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa wani lokaci yaran da iyayensu suke cin rani suke aiki a wurare masu nesa su kan jin kadanci,suna so su yi hira tare.Ban da wannan kuma tsohon Mr Wang Zhi ya kan fadakar da yaran a tunani,ya kwantar da hankalinsu. A cibiyar ba da taimakon ilimi,malaman koyarwa su kan ba da ilimi a dare yayin da yaran ke karatu da kansu,su kan ba da amsa ga yaran da kara musu ilimi.Ana tafiyar da harkokin cibiyar ba da taimakon ilimi kamar yadda ake tafiyar da harkokin gidan renon yara.An kula da yaran cibiyar wajen abinci da dakin kwana da ba da ilimi da dai sauransu. Da rana yaran su tafi makarantu su yi karatu,da tsakar rana da dare su koma cibiyar ba da taimakon ilimi su sami kulawa da Mr Wang Zhi ya nuna musu kamar kakaninsu.

Yar cibiyar Zhu Eenzhi tana karatu a jami'a a halin yanzu, amma a da koma baya take wajen karatu. Bayan da aka shiga da ita a cibiyar, ta yi kome yadda ya kamata wajen karatu da zama,ta sami kyakkyawr al'ada,ta samu ci gaba sosaia wajen karatu,daga bisani ta cimma burinta na shiga jami'a ta hanyar jarrabawa. Mr Wang Zhi ya bayyana cewa :" A ganina abun mafi muhimmanci shi ne mu fadakar da yara da su zama masu nagarta,sa'nnan su samu ilimi mai amfani. Wadannan abubuwa biyu suna da muhimmancin kwarai da gaske.kullum muna bin wannan ka'ida.mun dora muhimmanci kan mayar da su zama nagartattu, a sa'I daya kuma ba mu yi sassauci wajen ba su ilimi ba.Idan wani ya yi kuskure,mu yi masa suka yadda ya kamata kuma cikin lokaci.idan wani ya aikata wani abin kirki,mu kan yi masa yabo,mu karfafa kwarin gwiwarsa da ya ci gaba da kokarinsa. Yaran da ke cikin cibiyar suna zaman sakin jiki da kwanciyar hankali."

Cibiyar ba da taimakon ilimi ga yara ta shafe shekaru bakwai ke nan yau bayan da aka kafa ta a shekara ta 2001,yaran sama da dari bakwai suka yi zama a ciki,yanzu sun fita daga wannan cibiya zuwa wuraren waje da duwatsu sun shiga sana'o'I daban daban.Da ganin wannan sakamako,tsohon Mr Wang Zhi mai farin gashi wanda ke aiki tukuru rana da dare,ya yi farin ciki sosai. Ya waiwayi tarihin cibiyar na tsawn shekaru bakwai ya bayyana cewa :

"Ina son in yi wani abu domin amfanin zamantakewa da jama'a.Idan na ba da tallafi ga wani yaro,yaron ya samu 'yanci.Idan na ceci wani yaro,ya yi daidai na ceci wani iyali.Idan na ba da tallafi ga wani yaro a muhimmin mataki,wannan yana nufin cewa na ba shi taimako a duk rayuwarsa." Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na yau na zaman rayuwar Sinawa.Mun gode muku saboda kun saurarenmu.sai mako mai zuwa za mu sake saduwa.(Ali)


1 2 3