Cibiyar ba da taimakon ilimi ga yaran tana bin wata hanyar tafiyar da harkokinta a rufe.wato yaran dake cikin cibiyar su yi kome bisa wani tsarin da aka tsara dominsu,su yi karatu da wasa kuma hutu yadda tsarin ya tanada,idan wani daga cikin yana son ya fita sai ya yi rajista,haka kuma ga mai neman shiga. Da dare da akwai wadanda ke yin sintiri da kuma masu gadi.Ban da wannan kuma an gayyaci malaman koyarwa biyar wajen ba da darasi da ma'aikata guda hudu. Ya kuma kebe wani daki domin karanta mujaloli da jaridu,ya kuma saye injuna masu kwakwalwa da injin dabi da injin copy machine,da camera vidiyo,da kayan wasan dara da kwalayen wasa. Cibiyar ta shirya jarrabawa sau daya a wata. An kuma ba da kyauta ga wanda ya fi samun ci gaba wajen karatu. Ban da ilimin da ake bayarwa a cibiyar,ana kuma shirya wasanni iri iri domin yara ta haka kuwa za a karfafa ingancin yara daga dukkan fannoni.
Yarinya Liu Dan mai shekaru 16 da haihuwa tana zama a cibiyar ba da taimakon ilimi cikin dogon lokaci saboda iyayenta su kan ci rani suke aiki waje da kauyensu.Madam Bai Xiaohong,mamar Liu Dan ta gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa:
"wani yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali ya game gidan yara,yaran suna girma cikin lami lafiya,ba na tsoron wata matsala ta same su. Domin malaman koyarwa da ma'aikatan sun kula da yaran yadda ya kamata daga dukkan fannoni. Yaran ba su iya fita waje yadda suka ga dama ba,sun mayar da hankalinsu kan karatu suna cikin zaman lafiya.idan suna cikin iyalansu,sai kowace rana su yi tafiyar kilomita biyar ko shida zuwa gidan,idan su yi tafiya da kekunan hawa,hankalinmu ba a kwance yake ba.Ga shi a yau kome na tafiya daidai suna cikin tsaro mai inganci."
Liu Dan ta kammala karatunta a karamar makarantar middle,ta fara karatunta a babbar makarantar middle a garin gunduma daga watan Stumba na bana.Da ta waiwayo tarihinta a gidan ba da taimakon ilimi,ta yi farin ciki da cewa:"A hakika mun yi zaman jin dadi a gidan,da akwai aminana da dama a gida,mun kula da juna muna taimakon juna,muna fahintar juna.Mu kan yi nazari tare yayin da muke karatu,haka kuma mu kan yi hira da bayyana abubuwan dake cikin zukatanmu,munajin dadin zama kamar iyali daya ne muke ciki."
1 2 3
|