Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-05 15:51:52    
An fara yin amfani da sabbabin dakunan karatu a kasar Sin

cri

Don biyan bukatun bunkasuwar laburare na zamani, dukkan sabbabin dakunan karatu na laburaren kasar Sin suna da alama watau siganal, masu karatu za su iya zuwa tare da kamfutar hannu watau lap-top, kuma za su iya duba shafin Internet a ko ina. Haka kuma a dakunan karatu, an dana kamfuta 460, don bayar da hidima mai kyau ga masu karatu don su yi amfani da su. Kazalika kuma, sabbabin dakunan karatu na laburaren kasar Sin sun samar da tashar karatu da aka siffanta kamar ainihin dakunan karatu, idan masu karatu sun tsaya a gaban babbar naurar nuna hoto watau Screen, za su iya karanta littattafai kuma za su iya daukar littatafai, a can ne za su karanta littatafai kuma za su iya canja su. Babban injiniya na dakunan karatu na laburaren kasar Sin Wu Bin ya bayyana cewa, wannan tashar karatu da aka siffanta kamar ainihi karatu, za ta iya rage wahalar lallacewar naurar hoton, a sa'i daya kuma za su iya inganta sha'awar yara. Ya bayyana cewa,

"Mun yi amfani da sabuwar fasaha ta siffanta ainihin cibiyar karatu, an yi amfani da hoton video don siffanta ayyukan da hannu ya yi, kuma zai kawo sauki yayin da ake karatu, daga bisani kuma, za a yi amfani da wannan fasaha wajen dakunan karatu na yara, kuma za a yi amfani da su su kara ilmi wajen fahimtar sabbabin fasahohi"

Dadin dadawa kuma, laburaren kasar Sin ya samar da tsarin zamani na dubawa GPS yadda masu karatu za su iya karanta dukkan littatafain da suka so duba a cikin kamfuta, nan take, tsarin GPS zai nuna littafin da ake so, haka kuma zai ba da jagoranci ga wurin da aka ajiye shi, don taimaka wa masu karatu don su iya samun wannan littafi cikin sauki.

A cikin wani yankin da aka kebe don siffanta ainihin laburare, akwai wata babbar na'ura da tsawonta ya kai mita 7 kuma fadinta ya kai mita 3, wannan ita ce na'ura mafi girma a duniya. Yayin da manema labaru suka tsaya kafin wannan babbar kariya, za su iya yin amfani da ita dan kai ziyara a sabbabin dakunan karatu na laburare, kuma za a kashe mitoci 20 ana ziyara a dukkan laburaren.

Bugu da kari kuma cikin sabbabin dakunan karatu an kafa wani laburaren makafi na zamani, mataimakin direkta na laburaren, Mr. Li Chunming ya bayyana cewa:

"Laburaren makafi na zamani ya yi amfani da littatafai na zamani da kide-kide, sabo da haka makafi suna sha'awarsu. Yayin da makaho suke karatu, za su iya karanta labaru cikin kundin bayanai na nau'ra mai kwakwalwa watau Software don gane abubuwan da suka rubuta a kan kariya"

Sabbabin dakunan karatu na kasar Sin sun samar da ci gaba ta fannin kimiyya da fasaha, abin da ya fi baiwa manema labaru mamaki kuma abin da ya fi faranta ran masu karatu shi ne, an nuna "Sikuquanshu" watau "littatafan da aka kasa kashi 4 da suka hada da dukkan muhimman littatafan kasar Sin" a sababin dakunan karatu na laburaren kasar Sin, da ma, an taba nuna shi sau biyu ne kawai, ga shi yanzu masu sha'awar kallo za su iya duba dukkansu a sababbin dakunan karatu na kasar Sin.

Sabo da wadannan littatafai sun yi tsada sosai, masu karatu ba su iya taba su, amma ga shi yanzu ta taga ma, masu karatu za su iya kallon shi daga dukkan fannoni.

Masu karatu sun nuna cewa, bayan da aka nuna "Sikuquanshu" a sabin dakunan karatu na laburaren kasar Sin, hakan ya sanya sabbabin dakunan karatu masu cikakkiyar fasaha, suna na dogon tarihi, kuma ya fitar da matsayinsu na laburaren kasar Sin.


1 2 3