Kwanakin baya, an bude sabon gidan karatu na kasar Sin, wannan ya nuna cewa, birnin Beijing zai mallaki gidan karatu mafi girma na uku a duniya.
Laburaren kasar Sin yana yammacin birnin Beijing, inda ke da manyan jami'o'i da dama, kuma da ma, an fara gina shi a shekarar 1909 kuma a wancan lokaci, aka kira shi "dakin karatu na Beijing", ya zuwa shekarar 1998, an canja sunansa zuwa "laburaren kasar Sin", wannan laburare da ke da littatafai mafiya yawa, ya jawo hankulan masu karatu da dama. Ministan al'adu na kasar Sin Mr. Cai Wu ya yi jawabi a gun bikin bude wannan sabon gidan karatu na kasar Sin, ya bayyana cewa:
Laburaren kasar Sin da ake ginawa a shekarar 1909, ya zama tamkar wata gada da ta hada kasar Sin da kasashen waje, kazalika kuma ta hada al'adu na gargajiya da na zamani, ya zuwa yanzu, yawan littatafin da aka ajiye a cikin wannan laburare ya kai miliyan 26, kuma yana matsayi na 5 a dukkan laburaren kasashen duniya.
Bana shekaru 99 ke nan cif da aka gina laburaren kasar Sin, Sin ta zuba jari da yawansa ya kai biliyan 1.3 wajen gina sabbabin wannan sabon gidan karatu, wanda ya sanya fadin laburaren kasar Sin ya kai murraba'in kilomita dubu 250, yana matsayi na 3 a duniya.
1 2 3
|