Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-05 15:51:52    
An fara yin amfani da sabbabin dakunan karatu a kasar Sin

cri

Sabon gidan karatu na kasar Sin yana da hawa 8, wasu 3 suna kasa, sauran 5 suna sama, fadinsa ya kai muraba'in kilomita dubu 80, sun kasu kashi 3, kuma su ne na kasa da na tsakiya da na sama. A kasa, an yi ado mai siffar wani littafi, na tsakiya kuma shi ne wani yanki da aka kebe musamman domin yin hidima mai kyau ga masu karatu, don su yi karatun. kazalika kuma a wannan hawa, hasken rana yana haska jikin masu karatu ta taga, kuma masu karatu za su iya samun ilmi ta karanta labaru tare da cin moriyar hasken rana. Na sama kuma shi ne, wani wurin da aka kebe domin alamantar makomar kimiyya da fasaha.

Bisa bayanin da shugaban laburaren kasar Sin Zhan Furui ya bayar, an ce, sabon gidan karatu yana da kujeru 3000, a ko wace rana, zai iya karbar mutane 8000, kuma zai iya bayar da hidima mai kyau ga masu karatu.

Za mu yi amfani da hidima ta gargajiya da ta zamani wajen kawo sauki ga masu karatu, don bayar da hidima mai kyau ga masu karatu, haka kuma za mu yi amfani da dandamalin laburare na zamani wajen bayar da bayanan littatafai ga masu karatu na Sin da na duniya, don su cin moriyar ala'dun kasar Sin mai dogon tarihi.

Dandamalin laburare na zamani da aka yi amfani da fasahar zamani ta digital a Turance, yana da wata nau'rar adana bayanai a tashar Internet, laburaren digital ya riga ya samar da littafai ta hanyar zamani watau E-book da yawansu ya kai dubu 720 ga masu karatu, masu karatu za su iya karanta littatafai ta Internet. Wannan shi ne daya daga manyan matakan da sabon laburaren ya dauka wajen taimaka wa masu karatu.


1 2 3