Amma duk da haka, saboda tabkin Wucaichi yana kasancewa a wuri mai tsayin mita dubu 4 ko fiye a matsayin teku, shi ya sa ba dukkan mutane ba ne suke iya isa tabki da kafarsu. Kou Yahui, mai kula da harkokin shiyyar Huanglong ya bayyana cewa, yanzu sun riga sun fito da dabarar taimakawa matafiya. Ya ce:
"A shekarar da muke ciki, mun shimfida hanyar zamani wato ta hanyar hawa kebir daga gindin babban tsauni zuwa kololuwar babban tsaunin, ta haka matafiya za su iya kallon tabkin Wucaichi. Sa'an nan kuma, mun gina tasoshi 5 na samar da iskar Oxygen ba tare da biyan kudi ba a hanyar hawan babban tsaunin, ban da wannan kuma, muna nan muna gina saura 2, za mu bai wa matafiya iskar Oxygen ba tare da biyan kudi ba. " 1 2 3 4
|