Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-04 15:48:06    
Ziyarar Aljannar da ke duniyarmu

cri

In an tabo magana kan lardin Sichuan na kasar Sin, watakila masu sauraronmu ba ku san shi sosai ba, amma in an tabo magana kan dabbar Panda, to, kowa ya kan nuna soyayya ga irin wannan dabba mai kyan gani. Ana samun ta ne a lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin.

Masu sauraro, baya ga dabbar Panda, akwai sauran abubuwa masu ban sha'awa a Sichuan, idan kuna son ku kara saninku kan Sichuan daga dukkan fannoni, to, don allah ku kasa kunne ku ji shirinmu na musamman. Tun daga yau za mu fara watso muku shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici ta 'kai ziyara ga kyakkyawan lardin Sichuan' ta rediyo da kuma internet. Muna jiran amsoshinku.

Kamar yadda muka yi a da, a karshen shirinmu na ko wane karo, za mu gabatar muku da tambayoyi 2.

To, masu sauraro, muna fatan za ku sami maki mai kyau a cikin gasar.

In mutum ya kai wa lardin Sichuan ziyara, amma bai je kwarin Jiuzhaigou da kuma wurin shakatawa na Huanglong ba, to, a ganinsa, ya yi kama da rasa ganin abubuwa masu ban sha'awa. Amma duk da haka, in ya yi yawon shakatawa a wadannan wurare biyu, to, zai manta da komawa gida. Yau ma za mu kai ziyara ga wadannan wurare 2 da Sinawa su kan mayar da su tamkar Aljannar da ke duniyarmu.

Kafin mu fara shirinmu na yau, da farko dai, za mu gabatar muku da tambayoyi 2, su ne, ko asalin sunan kwarin Jiuzhaigou yana da nasaba da kauyuka 9 na kabilar Tibet da ke cikin wannan kwari ko a'a. Na biyu, ko an tanadi kwarin Jiuzhaigou da wurin shakatawa na Huanglong a kan takardar sunayen wuraren tarihi na halitta na duniya ko a'a? Masu sauraro, sai ku karkade kunnuwanku don jin abubuwan da muka shirya, ta haka za ku amsa tambayoyin da muka yi muku.

Kwarin Jiuzhaigou yana cikin shiyya mai cin gashin kanta ta kabilun Tibet da Qiang ta Aba da ke yammacin lardin Sichuan na kasar Sin, siffarsa ta yi kama da harafin Turanci na 'Y'. An nada wannan kwari mai zurfin kilomita fiye da 40 da sunan kwarin Jiuzhaigou saboda ya kasance da kauyuka 9 na kabilar Tibet a wurin.


1 2 3 4