Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-04 15:48:06    
Ziyarar Aljannar da ke duniyarmu

cri

Mr. Nerohem da ya zo daga kasar Isra'ila yana son yin bulaguro a duk fadin kasar Sin. A shekaru da dama da suka wuce, ya taba kai ziyara ga biranen Beijing da Shanghai da kuma lardunan Zhejiang da Shaanxi da sauran wurare, ma iya cewa, ya san al'adun gargajiya na kasar Sin da kuma kyan ganin ni'imtattun wurare a kasar Sin. Amma bayan da ya yi bulaguro a kwarin Jiuzhaigou, ya nuna mamaki kan kyan ganin wannan kwari da ya sha bamban da saura. Ya ce:

"Wannan kwari wuri ne mafi kyan gani a kasar Sin. Ban taba ganin irin ni'imtattun wurare masu kyan gani haka a sauran wurare ba. Dukkan abubuwan da na gani a wurin sun sha bamban da saura."

Kwarin Jiuzhaigou yana ba da mamakinsa ne saboda ruwa. Ruwa tamkar rai ne gare shi. Akwai tabkuna manya da kanana fiye da 100 masu launuka iri daban daban a cikin wannan kwari, mazauna wurin 'yan kabilar Tibet sun kira su "Haizi" wato 'ya'ya maza na teku a Turance.

Ruwan da ke cikin wadannan tabkuna na da tsabta sosai, har ma an iya ganin kananan duwatsu da ciyayin ruwa da kuma matattun rassan itatuwa a gindin tabkunan. Launukan ruwan suna da iri daban daban, kamar shudi da kore da kuma rawaya.

Mr. Morishita Sadamasa, dan kasar Japan ya yaba wa tabkuna sosai bayan da ya more wa idonsa da kallon wadannan tabkuna masu kyau, ya ce:

"Na taba kallon wurare masu ni'ima na kwarin Jiuzhaigou ta talibijin a kasarmu ta Japan, amma bayan ganin wurare masu ni'ima a nan, ina ganin cewa, sun fi kyan gani bisa abubuwan da na taba gani a kan talibijin. Akwai irin wadannan tabkuna a kasarmu, duk da haka wadanda ke cikin kwarin Jiuzhaigou sun fi kyan gani."

An samu ruwa mai launuka daban daban a kwarin Jiuzhaigou bisa ikon Allah. Dalilin da ya sa haka shi ne domin tsarin kasa na Karst a kwarin Jiuzhaigou da kuma tsirran Algae iri-iri fiye da 200 da aka samu a cikin tabkuna.

Ban da ruwan da ke cikin tabkunan Haizi, suna gangara sannu a hankali, an samu jerin magangarar ruwa 17 a cikin kwarin Jiuzhaigou. Ba su da tsayi sosai, amma suna da fadi sosai, idan aka hango daga nisa, sai ka ce labule na ruwa mai fadi ya rufe hayi duka, yana da kyaun gani, kuma ya ba mutane mamaki sosai.

Shi kwarin Jiuzhaigou, wani wuri ne da Sinawa suka mayar da shi kamar aljannar da ke duniyarmu. A shekarar 1992, hukumar ilmi da kimiyya da al'ada ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta tanadi kwarin Jiuzhaigou a cikin 'takardar sunayen wuraren tarihin halitta na duniya'.


1 2 3 4