Kazalika kuma, wannan kwararriya ta gabatar wa masu sauraronmu da wasu dakunan cin abinci da suka gasa agwagi ta sabbin hanyoyi. Ta gaya mana cewa, wadannan sabbin dakunan cin abinci sun mai da hankulansu kan wuraren da za su samarwa masu cin abinci, sun kuma kayatar da kansu ta hanyoyin musamman, ta haka, matafiya daga kasashen waje sun iya gane bambanci. Madam Chen ta ce:
'Akwai wani dakin cin abinci mai suna Quanyaji, inda aka gasa agwagi da yawa. Sa'an nan kuma, wurin da aka ci abinci a ciki yana da muhimmanci sosai, ya zama wata irin al'adu. Dakin cin abinci na Tiandiyijia da ke kusa da titin Nanchizi aka samu shi ne bayan da aka yi kwaskwarima kan wani gidan kwana mai fasali hudu irin na gargajiya na Beijing. A da watakila dattijai sun taba zama a wannan gidan kwana mai fasali hudu irin na gargajiya na Beijing, shi ya akwai abubuwan tarihi da yawa a ciki, haka kuma, zane-zanen da ke kan bango sun nuna halayen musamman irin na kasar Sin.'
Mai yiwuwa ne mutanen da suka zo kasar Sin ziyara a karo na farko daga kasashen waje za su gamu da matsala, wato ko cin abinci a dakin cin abinci na Quanjude domin kara saninsu kan al'adun kasar Sin mai dogon tarihi, ko kuma cin abinci a dakin cin abinci da ake gasa agwagi ta sabbin hanyoyi domin kara fahimta kan kasar Sin na zamani. Amma duk da haka, masu sauraro, in kun kawo wa kasar Sin ziyara a wannan lokacin zafi, to, tabbas ne za ku ci wannan shahararren abinci wato gasassun agwagi irin na Beijing. (Tasallah) 1 2 3 4
|