Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-04 15:44:00    
Cin gasassun agwagi irin na Beijing

cri

A matsayin dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi mai dogon tarihi, sunan Quanjude na kusan kasancewa alamar musamman da ke wakiltar gasassun agwagi irin na Beijing. Game da halayen musamman na gasassun agwagi da ake samarwa a dakin cin abinci na Quanjude, kullum Mr. Wang ya ji alfahari sosai, ya ce:

'In bakinmu sun ga wata gasasshiyar agwagwa mai kiba da yawa da muke samar musu a tebur, su kan rasa abin da za su yi, kukunmu su kan yanke naman agwagwar tamkar yadda warkokin nama ke nan. In wani ya nuna sha'awa sosai, to, ya iya yanke naman agwagwa da kansa, ta haka, zai kara jin farin ciki bisa cin naman da ya yanke.'

A dakin cin abinci na Qungjude, a kan yanke naman gasasshiyar agwagwa ta hanyoyi 3, ciki har da tsalar naman agwagwar tare da fatarta. Wang Rong ya gaya cewa, a da ba a yanke namen gasasshiyar agwagwa zuwa tsala ba, dalilin da ya sa haka shi ne domin:

'A shekarun 1960, Zhou Enlai, tsohon firayim ministan kasar Sin ya gayyaci bakin da suka zo daga kasashen waje don ci abinci a dakin cin abinci na Quanjude. Baki daga kasashen waje su kan yi amfani da cokali mai yatsu, ba su iya amfani da tsinke wajen cin abinci ba. Shi ya sa Mr. Zhou ya shawarci a yanke naman gasasshiyar agwagwa zuwa tsala, ta haka ana iya nannade naman gasasshiyar agwagwa da waina mai laushi cikin sauki, kuma ana iya ci cikin sauki.'

Tun daga nan aka gaji irin wannan hanyar yanke naman gasasshiyar agwagwa a dakin cin abinci na Quanjude. Biyan bukatun masu cin abinci daga kananan fannoni ya nuna cewa, jama'ar Sin suna nuna wa baki kyakkyawar maraba.

Gada fasahohi da hanyoyi da kuma al'adun gargajiya tare da samun kirkire-kirkire ita ce muhimmiyar hanya da dakin cin abinci na Quanjude ke bi wajen ci gaba da yin suna a gida da kuma waje a cikin shekaru 100 ko fiye bayan kafuwarsa. Mr. Wang ya kara da cewa:

'Alal misali, wata agwagwa ta kan bukaci kiwonta kwanaki 45 domin cancanta gasawa a yanzu, a maimakon kwanaki 60 a da. Kuma muna tsara tsauraran ma'auni kan zaben danyun abubuwa daga karin fannoni. Ban da wannan kuma, mu kan dauki mintoci 50 zuwa awa 1 wajen gasa wata agwagwa a maimakon mintoci 45 a da. Ta haka, kitse da kuma miya da ke cikin agwagwar za su kara hadewa da juna bayan da aka gasa ta, agwagwar za ta kara dadin ci.'


1 2 3 4