Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-04 15:44:00    
Cin gasassun agwagi irin na Beijing

cri

A watan Yuli na wannan shekara, dakin cin abinci na Quanjude ya kaddamar da wata takardar abinci ta wasannin Olympics. Mr. Wang ya yi karin bayani da cewa, an dauki kusan shekara guda domin fito da wannan takarda. Dakin cin abinci na Quanjude ya kyautata abinci da yawa da ke kan wannan takarda bisa dandanon da mutanen waje suke so. Ya ce:

'Bisa fasahohinmu, mun fara ajiye wasu kayan kamshi da a kan yi amfani da su cikin abinci irin na yammacin duniya a cikin abincin da muke samarwa. Alal musali, mun dafa hantar agwagwa tare da man shanu. Nufinmu shi ne biyan bukatun mutanen kasashen waje da kuma kara saninsu kan abinci irin na kasar Sin da kuma nuna musu al'adun kasar Sin mai dogon tarihi ta fuskar abinci.'

A kwanan baya, dakin cin abinci na Quanjude ya yi wa rassansu kwaskwarima domin karbar karin masu cin abinci. Sa'an nan kuma, ya horar da sabis a fannonin da abin ya shafa, ya kuma yi kokarin kyautata matsayinsu a fannonin tuntubar masu cin abinci cikin Turanci da kuma ba da hidima.

Dakin cin abinci na Quanjude yana fatan ko wane mai cin abinci zai fahimci Sinawab da ke son baki da kuma dumama zukatunsu. Baya ga Turanci, sabis da ke aiki a cikin wannan dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi sun kuma koyi al'adun gargajiya da ake bi a yankuna da kasashe na duk duniya da kuma abubuwan kunya, har ma da yin magana ta hanyar alamu.

Yanzu abincin kwalama suna samun saurin bunkasuwa, amma duk da haka ana ci gaba da gasa agwagi ta hanyar gargajiya wajen samar da gasassun agwagi irin na Beijing. Ana samun karin dakunan cin abinci da suka yi kama da dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi mai suna Quanjude a Beijing. Dakin cin abinci na sayar da gasassun agwagi mai suna Dadong na daya daga cikin irin wadannan dakunan cin abinci, shi ma ya fara kafa rassansa a Beijing. Chen Qianzhu, wata kwararriya ce a fannin al'adun abinci. Dangane da irin wadannan dakunan cin abinci na sayar da gasassun agwagi, ta bayyana ra'ayinta bayan da ta kwatanta su. Ta ce:

'Dakin cin abinci na Dadong ya fi mai da hankali kan biyan bukatun mutanen kasashen waje, ko da yake ya bi hanyar gargajiya wajen gasa agwagi, amma ya nuna bambanci a naman agwagi. A ganina, naman gasassun agwagi da ake samarwa a dakin cin abinci na Dadong yana da dadin ci sosai kamar yadda naman gasassun agwagi da ake samarwa a dakin cin abinci na Quanjude yake.'


1 2 3 4