Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-03 17:17:06    
Mafarki na kamfanin Lenovo na kasar Sin

cri

A hakika dai, ba ta wannan hanya kadai kamfanin Lenovo ya shiga harkokin gasar wasannin Olympic ta Beijing ba. Kamfanin Lenovo ya kuma samar da injuna masu kwakwalwa da kudade da fasahar tabbatar da aikin injuna masu kwakwalwa ga gasar wasannin Olympic ta Beijing da kwamitocin wasannin Olympic na kasashe da yankuna fiye da 200 da kungiyoyinsu na wakilan wasannin Olympic. A waje daya kuma, ya kafa tsarin watsa labaru a cikin dakuna da filayen motsa jiki 38 da ke birane 7 domin kafa wani dandalin sadarwa na gasar wasannin Olympic ta Beijing. Mr. Yang Yuanqing, shugaban hukumar direktoci na kamfanin Lenovo ya ce, "Ba yolar wuta kawai kamfanin Lenovo ya yi wa gasar wasannin Olympic ta Beijing ba, hatta ma mun samar da dukkan injunan IT na fasahar sadarwa da yawansu ya kai fiye da dubu 30 ga gasar."

Tun daga lokacin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Beijing zuwa lokacin rufe wannan gasa, wadannan injunan da kamfanin Lenovo ya samar wa gasar sun yi aiki kamar yadda ake fata. Wannan ya bayyana cewa, injuna da kayayyakin da kamfanonin kasar Sin suka samar suna da inganci. Bugu da kari kuma, kamfanin Lenovo ya aika da masana harkokin fasaha su 580 domin ba da tabbaci ga aiwatar da tsarin sadarwa ba tare da kowane aibu ba. Kuma sun tsara shirin tabbatar da aiwatar da aikin injuna domin tabbatar da kaucewa samun akasi. Ya kamata mu ce, ba za a iya mantawa da gudummowar da kamfanin Lenovo ya bayar ba lokacin da ake murnar nasarar da aka samu a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ko shakka babu, ayyukan da kamfanin Lenovo ya yi sun kuma kara yaduwar alamar kayayyakinsa a duk fadin duniya. Mr. Yang Yuanqing yana ganin cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta kawo wa kamfanin Lenovo sauye-sauyen da ba a taba gani ba a da. "Sakamakon da kamfanin Lenovo ya samu bayan da ya tallafawa gasar wasannin Olympic ta Beijing yana nan a bayyane sosai. Yau da shekaru 4 ko 5 da suka gabata, yawan kudaden da muka samu bai wuce dalar Amurka biliyan 3 kawai ba, amma yanzu wannan adadi ya kai kusan dalar Amurka biliyan 17. Bugu da kari kuma, yawan ribar da muka samu a shekarar da ta gabata ya ninka sau ukku idan an kwatanta shi da na yau da shekaru 4 ko 5 da suka gabata. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, mun yi amfani da wannan dama mun yi aikin yada alamar kayayyakinmu a duk duniya da kyau." (Sanusi Chen)


1 2 3