Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-03 17:17:06    
Mafarki na kamfanin Lenovo na kasar Sin

cri

Sabo da haka ne, kamfanin Lenovo na kasar Sin ya tsai da kudurin tallafawa gasar wasannin Olympic ta Beijing. Amma idan wani kamfani yana son zama abokin hadin guiwa na wasannin Olympic a duk fadin duniya, dole ne yawan tallafin kudin da ya biya ya kai miliyoyin dalar Amurka. Sakamakon haka, wasu mutane suna nuna shakku kan ko wadannan kudade za su isa bukatar da mai ba da tallafi ke nema? A hakika dai, a matsayin wani kamfanin da aka kafa shi yau fiye da shekaru 20 da suka gabata, kamfanin Lenovo ya kan samu rinjaye kan fasahar harhada injuna masu kwakwalwa na mutum a cikin masana'antun harhada injuna masu kwakwalwa na duniya. A shekarar 1994, kamfani na Lenovo ya samu nasarar cinikin takardun hannun jari a kasuwar harhada kudade ta Hongkong. Sannan a shekara ta 2005, wannan kamfani na Lenovo na kasar Sin ya kashe dalar Amurka biliyan 1.25 ya sayi harkokin injuna masu kwakwalwa na kamfanin IBM wanda ya fi suna a duk fadin duniya wajen samar da injuna masu kwakwalwa na mutum. Sakamakon haka, yawan injuna masu kwakwalwa da yake sayarwa a kasuwannin duniya ya kai matsayi na ukku a biye da kamfanin Dell da kamfanin HP. Ana tsammani cewa, bayan da kamfanin Lenovo ya tallafawa gasar wasannin Olympic ta Beijing, ko shakka babu kamfanin Lenovo ya samu karfi wajen neman bunkasuwa a kasuwannin duk duniya. Mr. Yang Yuanqing, shugaban hukumar direktoci na kamfanin Lenovo ya ce, "Wannan ne karo na farko da aka yi gasar wasannin Olympic a kasar Sin. A matsayin wani kamfanin kasar Sin, muna tsammani muna da hakkin bayar da gudummowarmu. A waje daya kuma, gasar wasannin Olympic wani kyakkyawan wuri ne da ake nuna wa duk duniya alamar samfurin Lenovo, musamman bayan da muka harhada harkokin PC na kamfanin IBM, yana da muhimmanci sosai mu zama wani kamfanin da ke neman bunkasuwa a duk fadin duniya."

Sabo da haka, a watan Maris na shekara ta 2004, kamfanin Lenovo na kasar Sin ya zama abokin hadin guiwa na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa a duk duniya. Ita ce masana'antar kasar Sin ta farko da ta samu irin wannan iko. Bayan da kamfanin Lenovo ya samu wannan iko, ya yi dimbin ayyuka domin gasar wasannin Olympic ta Beijing, alal misali, ya tsara samfurin yolar wuta ta gasar wasannin Olympic ta Beijing. A cikin zane-zanen yolar wuta iri na 388 da aka gabatar, yolar gajimare mai fatan alheri da kamfanin Lenovo ya zana ta ci nasara sabo da tana nune-nunen al'adun al'ummar Sinawa, kuma tana dacewa da halin zamani da ake ciki yanzu. Mr. Yao Yingzhu, babban mai zana wannan yola shi ne mataimakin babban direktan kamfanin Lenovo. A ran 8 ga watan Agusta, lokacin da aka kunna babbar yola a gun bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Beijing a filin wasannin motsa jiki na kasar Sin, Mr. Yao Yingzhu yana gidansa yana kallon talibijin kuma yana sauraran ihun da aka yi a waje. A hukunce ne aka bude wannan gagarumin bikin da wannan babban mai zana yolar wuta ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ya jira. Mr. Yao ya ce, "A hukunce ne aka soma wannan gagarumin biki. Ihun da aka yi a gidaje daban daban ya kawo gidana. Sun sa kaimi ga kasar Sin. A wancan lokaci, nan da nan ne na gane cewa, wannan babbar yolar wuta ta ta da hankalin dimbin mutane. An burge ni a cikin zuciyata a wancan lokaci."


1 2 3