An riga an rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekara ta 2008. Lokacin da aka yi wannan gasa, an kuma shirya wata gasa daban, wato gasar talla. A matsayin daya daga cikin masana'antun da suka fi tallafawa gasar wasannin Olympic ta Beijing, kamfanin harhada injuna masu kwakwalwa kirar Lenovo, wato kamfani mafi girma a nan kasar Sin wajen samar da injuna masu kwakwalwa ya samu babbar moriya a gun wannan gasa. Yanzu wannan kamfani ya riga ya shiga sunayen masana'antu da kamfanoni 500 wadanda suka fi girma da karfi a duk duniya da mujallar "Fortune" ta kasar Amurka ta zaba kuma ta bayar a kan shafin yanar gizo a shekara ta 2008. Yawan kudaden shiga da kamfanin Lenovo na kasar Sin ya samu ya kai dalar Amurka biliyan 16.8. Amma yau da shekaru 4 da suka gabata, yawan kudaden shiga da wannan kamfani ya samu a shekara daya ya kai dalar Amurka biliyan 3 kawai.
A matsayin wani gagarumin bikin wasannin motsa jiki da ke jawo hankalin duk duniya, gasar wasannin motsa jiki ta Olympic da aka saba shiryawa a kowane shekaru 4 ta kan jawo hankalin biliyoyin 'yan kallo na duk duniya. Sabo da haka, ikon tallafawa gasar wasannin Olympic ya zama ikon da manyan masana'antu da kamfanoni suke kokarin neman samu. A gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, an fi mai da hankali wajen neman wannan iko. Mr. Zhu Xiaoming, shugaban kamfanin Taidu na kasar Sin, wanda ya dade yana nazarin yadda ake yin cinikayya a gun gasannin wasannin motsa jiki ya ce, "Yawan kasashen da suka halarci wannan gasar wasannin Olympic ta Beijing ya fi yawa a kan tarihin gasannin wasannin Olympic. Idan an tallafa wa gasar wasannin Olympic, za a iya ganin cewa, wadanda suka tallafawa gasar wasannin Olympic suna da karfi da arziki."
1 2 3
|