
Mataimakin firayin ministan kasar Sin Mr. Wang Qishan ya ce,
'Za mu zurfafa hadin kanmu a fannonin cinikayya da zuba jari, domin tabbatar da kawo karshen aikin gina yankin cinkayya maras shinge da ke tsakanin Sin da kungiyar ASEAN. Za mu kara hada kanmu a tsakanin kananan yankunanmu. Cikin yakini ne, kasar Sin ta nuna goyon baya ga ayyukan dakulewar tattalin arzikin kungiyar ASEAN wuri daya, da gaggauta gina yankin tattalin arziki da ke tekun Bac Bo. Za mu tinkari kalubale tare, kasar Sin za ta dauki nauyin da ke bisa wuyanta, da kara samun daidaituwa da gama kai da kasa da kasa na kungiyar ASEAN a fannonin kudi, da makamashi, da kare muhalli, da samun hatsi yadda ya kamata da dai sauransu, ta yadda za mu iya tabbatar da samun zaman karko da bunkasuwar tattalin arziki da sha'anin kudi yadda ya kamata a yankinmu.'(Danladi) 1 2 3
|