A gun bikin bude taron baje koli na wannan karo, babban sakataren kungiyar ASEAN Mr. Surin Pitsuwan ya yi kira ga Sin da kungiyar ASEAN da su kara ingiza hadin kansu, domin tinkarar tabarbarewar halin da ake ciki dangane da rikicin harkokin kudi da ake fuskanta a halin yanzu. Ya ce,
'A halin yanzu da muke ciki, tabarbarewar rikicin harkokin kudi na duk duniya ya matsa wa bunkasuwar tattalin arziki na kasa da kasa lamba sosai. Ba za mu iya tinkarar kalubale yadda ya kamata ba, sai dai in muka dinga hada kanmu, da kyautata tsarin rarraba albarkatai, da inziga dunkulewar yankinmu wuri daya. Na yi imani cewa, halin da muke ciki yanzu ya fi na shekaru 10 da suka wuce kyau. Kungiyar ASEAN da Sin za mu iya rage illar da rikicin harkokin kudi ya haddasawa tattalin arzikinmu ta hanyar hada kai a tsakaninmu.'
1 2 3
|