An bude bikin baje koli a karo na 5 tsakanin Sin da kungiyar kasashen masu kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN a takaice a ran 22 ga watan a birnin Nanning, babban birnin jihar Guangxi ta kabilar Zhuang da ke da ikon tafiyar da harkokinta ta kasar Sin. Game da tabarbarewar halin da ake ciki a halin yanzu dangane da harkokin kudi da tattalin arziki, manyan jami'ai na Sin da kungiyar ASEAN da ke halartar taron, duk sun bayyana buri daya na kara hada kai a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da kokartawa tare domin tinkarar ricikin harkokin kudi.
1 2 3
|