Wajen manoma, bikin shigowar yanayin kaka ya bayyana cewa, yana shafar girbin da za su samu a duk shekarar. Da akwai karin magana da ya bayyana tasirin da ruwan sama da yanayin sararin samaniya suka yi wa girbin da za a samu. Alal misali, in ana ruwa a yanayin kaka, sai za a sami zinariya a ko'ina, wato, in ana ruwa a yanayin kaka, to za a sami girbi mai armashi. Wannan ya nufi cewa, ruwan sama da ake yi a yanayin kaka na da daraja sosai. Akwai karin magana da ya tsinkayi yanayin sararin samaniya na nan gaba ta hanyar nufin da iskar ta yi a yanayin kaka, alal misali, kafin yanayin kaka, in an tashi iska daga arewa, to, za a sami ruwa bayan yanayin kaka, in ana kada iska daga arewa, to ruwan kogi zai kare bayan yanayin kaka.
A ganin 'yan kabilar Tibet, yanayin kaka ba ma kawai shi ne yanayin samun girbi mai armashi ba, hatta ma shi ne yanayi mai kyau da aka yi wanka, za a iya shawo kan ciwace-ciwace da bala'i. A jihar Tibet da lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, in an shiga watan Augusta, sai an yi bikin maraba da yanayin kaka, a wannan lokaci, an yi wasannin Tibet da addu'ar addini da wanka da sauran aikace-aikace, dukkan wadannan sun bayyana cewa, mutane suna kaunar yanayin kaka sosai.(Halima) 1 2 3
|