Game da yanayin kaka, ilmin yanayin sararin smaniya ya tsai da cewa, in kwatankwacin zafi na ranaku 5 a jere bai kai centigrade 22 ba, ana iya cewa, yanayin kaka ya soma shigowa bayan yanayin zafi. Amma a hakika dai ne, kasar Sin kasa ce makiyayya, zafin wurare daban daban da yanayin sararin samaniyarsu suna da bambanci sosai, sa'anan kuma an sami tasirin kara dumamawar yanayin sararin samaniya a duk duniya a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, a lokacin shigowar yanayin kaka, kwatankwacin zafin yanayin sararin samaniya na yawancin wuraren kasar Sin ya kuma ci gaba da kasancewa cikin zafin da ya kai centigrade 22 ko fiye. Muddin lokacin ya kai tsakiyar watan Satumba, sai yawancin wuraren kasar Sin sun shiga yanayin kaka a hakika. Saboda haka, a kasar Sin da akwai wani karin magana da ya bayyana cewa, yanayin kaka na da zafi tamkar yadda yanayin zafi yake yi. Ma'anar nan ita ce, bayan shigowar yanayin kaka, wani lokaci, a cikin wasu ranaku a jere, zafin yanayin sararin samaniya ya iya kai centigrade 35 zuwa 40 ko fiye, tamkar yadda damusa ta yi fushi sosai ba ji ba gani. Dalilin da ya sa ana zafi haka a yanayin kaka? Shi ne saboda yanayin kaka yana shigowa a kudancin kasar Sin daga tekun Pasific na yamma, amma wani lokaci yana kan koma arewacin kasar Sin, bisa halin nan ne, a sararin samaniya, hasken rana na da yawa, amma an yi karancin gizagizai , shi ya sa zafi ya kara karuwa. A hakika dai ne, a sauran wurare na duk duniya, ana kan samun halin da ake ciki na ci gaba da yanayin zafin da ba ya son wucewa ba. A kasashen Turai, ana cewa, irin yanayin sararin samaniya shi ne yanayin zafi na tsohuwa, a arewacin nahiyar Amurka, ana cewa, shi ne yanayin zafi na Indian.
1 2 3
|