A cikin shirinmu na yau, za mu yi bayani kan ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya na kasar Sin. Game da ranar bikin yanayin sararin samaniya, an bayyana cewa, bisa sauyawar yanayin sararin samaniya da yawan ruwan sama da ake samuwa da tsawon lokacin saukar jaura da dai sauran almomin halittu ne, aka raba shekara guda don ta zama matakan lokutan bayyana almomin yanayin sararin samaniya lokaci lokaci, ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya su ne ranakun somawar wadannan matakan lokutan bayyana almomin yanayin sararin samaniya. Tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya shi ne sakamakon da jama'ar zamani aru aru na kasar Sin suka samu a lokacin da suke duddubawa tare da yin nazari kan ilmin yanayin sararin samaniya . Wannan yana da tasiri mai muhimmanci sosai ga harkokin noma. Bisa bayanan da aka tanada, an rubuta cewa, a shekarar 104 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S), mutanen kasar Sin sun riga sun tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya, don tunawa da su sosai, mutanen zamanin da sun kuma tsara wakoki dangane da ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya.
Bikin shigowar yanayin kaka wato "Liqiu" na shekarar da muke ciki ya zo ne a ranar 7 ga watan Augusta, bikin ya bayyana bikin sauyawar yanayin sararin samaniya. Da akwai wani karin magana da ya bayyana cewa, iskar sanyi ya zo a ranar shigowar yanayin kasa. Ma'anar Liqiu ta bayyana cewa, yanayin zafi ya wuce, kuma yanayin kaka mai dan sanyi ya soma shigowa.
1 2 3
|