Madam Ralph ta jami'ar Illinois ta kasar Amurka ta buga wani rahoto a kan mujallar girman jarirai, inda ta nuna cewa, ita da abokan aikinta sun gudanar da wani bincike ga jarirai 93, kuma iyaye mata na jarirai 44 daga cikinsu sun taba shan taba lokacin da suke da ciki, haka kuma rabin wadannan iyaye mata sun taba shan taba fiye da kara 10 a ko wace rana. Daga baya kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, game da jariran da iyayensu mata suka taba shan taba kafin haihuwarsu, sun fi saukin tafiyar da harkoki ba kamar yadda ya kamata ba in an kwantata su da jariran da iyayensu mata ba su sha taba ko kadan ba kafin haihuwarsu.
Ban da wannan kuma manazarta sun nuna cewa, akwai bambanci a bayyane a fannin salon da a kan bi wajen tafiyar da harkoki da ke tsakanin jariran da iyayensu mata suka sha taba lokacin da suke da ciki da na wadanda ba su sha taba ba. Jariran da iyayensu mata suka sha taba lokacin da suke da ciki su kan sha wahaloli a fannin daidaita harkokin da suke tafiyarwa da kuma mayar da martani kan harkokin da ke faruwa lokacin da shekarunsu ya kai watanni 18 zuwa 24 da haihuwa. Ban da wannan kuma sun fi son yin amfani da karfi da rashin yarda da ra'ayoyin sauran mutane, da kuma rashin iya yin mu'amala da sauran mutane.(Kande Gao) 1 2 3 4 5
|