Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-20 17:04:33    
Manoma ka iya mika ikon daukar nauyi kan gonakai ta hanyoyi daban-daban a kasar Sin

cri

Jama'a, a matsayin wata babbar kasa ta noma, akasarin manoman kasar Sin da yawansu ya yi sama da miliyan 700 suna yin aikin kawo albarkar noma ne kan gonakai kalilan. Idan an tabbatar da burin tattara gonakai ta hanyar mika ikon karbar hayar gonakai, to zai yiwu za a samu karin karfin takara da kasar Sin take da shi a fannin gudanar da harkokin sha'anin noma, ta yadda manoma za su kara samun kudin shiga da kuma gaggauta raya biranen kasar.

Kazalika, Mista Zhao Yutian ya furta cewa, takardar da aka fito da ita a wannan gami ta yi nazarin gano wata hanya mai amfani da za a bi wajen kirkiro sabon tsarin kula da gonakai bisa tushen tsarin daukar nauyi bisa kwangila kan iyalin manoma a fannin samun gonakai. Yana mai cewa: " Kyale manoma su mika ikon karbar hayar gonakai da kuma gudanar da harkokin noma bisa babban sikeli, ko shakka babu zai yi kyakkyawan tasiri ga samun karin kudin shiga ga manoma. Ban da wannan kuma, irin sabon salon kasuwanni da za a bullo da su zai amfana ga manoma wajen samun karin kudin shiga". ( Sani Wang )


1 2 3