Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-20 17:04:33    
Manoma ka iya mika ikon daukar nauyi kan gonakai ta hanyoyi daban-daban a kasar Sin

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wata muhimmiyar takarda jiya Lahadi da zummar daukaka ci-gaban yunkurin gyare-gyare da bunkasa kauyukan kaksar. A cikin takardar din, fafau aka kyale manoma mika ikon daukar nauyi kan gonakai bisa doka. Sa'annan takardar ta yi tayin kafa kasuwannin mika ikon daukar nauyi kan gonakai a kauyuka da kuma kyale manoma bunkasa aikin kawo albarkar noma bisa wani matakin da ya dace. Wani kwararre a fannin sha'anin noma na kasar Sin ya fada wa wakilinu cewa, wannan takarda za ta ingiza yunkurin yalwata tattalin arzikin kauyukan kasar da kyau, da sa kaimi ga samun karuwar amfanin gona da kuma karin kudin shiga ga manoma.

An amince da wannan muhimmiyar takarda ne a gun cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da aka rufe yau da mako guda da ya gabata. Wannan takarda ta kasance kashi daya dake cikin tsarin rubanya yawan kudin shiga da kowane manomi zai samu a shekarar 2020 idan aka kwatanta shi da na shekarar 2008.


1 2 3