Jama'a, a karshen shekarar 1970 ne aka tabbatar da tsarin daukar nauyi kan iyalin manoma wajen karbar hayar gonakai a kauyukan kasar Sin. Wannan tsari ya tanadi cewa, Jama'a ne ke mallalkar gonakan kauyuka. Amma a iya rarraba wasu gonakai kalilan ga manoma don gudanar da harkokin noma bisa kwangila. Wassu dokokin shari'a da abun ya shafa na kasar Sin na wancan lokaci sun tabbatar da cewa ba a yarda da manoma su yi hayar gonakai ba ko mika su ga saura ko kuma mika ikon daukar nauyi ta sauran siffofi.
Wani masani ilimin tattalin arziki daga ma'aikatar noma ta kasar Sin, Mista Zhao Yutian ya bayyana ra'ayinsa cewa, a yanzu haka dai, gwamnatin kasar Sin ta kyale manoma su mika ikon daukar nauyi kan gonakai bisa doka; lallai cimma tudun dafawa ne aka yi wajen kwaskwarimar tsarin kula da gonakai na da. Hakan zai daukaka cigaban yunkurin bunkasa tattalin arizkin kauyuka a nan gaba. Mista Zhao yana mai cewa: "Wannan takarda na da ma'anoni guda biyu. Ma'ana ta farko ita ce an samu goyon baya ta fuskar manufa yayin da manoma suke mika ikon daukar nauyu kan gonakai bisa doka; Ma'ana ta biyu ita ce, takardar za ta inganta aikin kawo albarka a fannin tattalin arziki yayin da take kara shigo da jarin waje da kuma musanye-musanyen amfanin gona. Ko shakka babu tana da muhimmancin gaske ga bunkasa kauyukan kasar da kuma warware matsalolin dake shafar " kauyuka, da manoma da kuma sha'anin noma".
1 2 3
|