A nan kasar Sin, tsimin makamashi da rage fitar da hayaki mai guba ya riga ya zama wani sabon ma'auni da ka'ida ga masana'antun kera motoci, kuma dimbin masana'antun kera motoci na mai da ka'idar a matsayin tafarkinsu. Kamfanin kera motoci na Foton da muka ambata a baya, ya zo gaba a wajen bunkasa motoci masu amfani da sabbin makamashi a kasar Sin. A halin yanzu dai, ya shirya sosai wajen bunkasa motoci masu amfani da sabbin makamashi, ya kuma kafa cibiyar nazarin motocin. A shekarar 2007, babban dakin gwajin motoci masu amfani da sabbin makamashi na Foton wanda aka saka kudin Sin da yawansu ya kai miliyan 200 a ciki ya kafu.
Ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin, Wan Gang ya kuma fayyace cewa, nan da shekaru uku masu zuwa, ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin za ta gudanar da motoci 1000 masu amfani da sabbin makamashi a manyan birane 10, don su ba da misali, kuma birnin Beijing ma yana ciki. (Lubabatu) 1 2 3
|