Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-17 16:11:08    
Motoci da sabbin makamashi a kasar Sin

cri

A wannan mako za mu amsa tambayar malam Sanusi Isah Dankaba, mai sauraronmu daga garin Keffi, jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya turo mana, ya ce, masana'antar motoci na daya daga cikin muhimman masana'antun kasar Sin, duk da haka, ta hanyar kara samun mallakar motoci, matsalar karancin makamashi ta kara tsananta, shin a ganinku, me ya kamata Sin ta yi don daidaita wannan matsala?

To, malam Sanusi Isah Dankaba, muna maka godiya da kawo mana wannan tambaya, kuma tambaya ce mai ma'ana. A gaskiya, yayin da karancin makamashi da gurbacewar muhallin zama ya zamo wa kasashe daban daban tarnaki, bunkasa motoci da ke amfani da sabbin makamashi ya riga ya zama abin da masana'antun motoci na kasashe daban daban ke kokarin ganowa. A nan kasar Sin ma, haka ake yi. Tuni a watan Faburairu na shekarar 2006, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da takardar tallafawa bunkasa motocin da ke amfani da sabbin makamashi, haka kuma a cikin shirin bunkasa kimiyya da fasaha na Sin daga shekarar 2006 zuwa ta 2020, ta sanya motar da ake amfani da dan makamashi da sabbin makamashi a matsayin abin da ya kamata a bayar da fifiko a kansa.


1 2 3